Kano: Hukumar Tace Fina Finai Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa, Ta Yi Gargadi

Kano: Hukumar Tace Fina Finai Ta Haramta Bikin Ranar Kauyawa, Ta Yi Gargadi

  • Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ɗauki mataki kan bikin ranar Ƙauyawa da ake yi domin shagalin aure
  • Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ya sanar da haramta gudanar da bikin a faɗin jihar Kano baki ɗaya
  • Abba El-Mustapha ya buƙaci limamai, dagatai da suka ba da irin tasu gudunmawar wajen ganin an bi dokar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta sanar da haramta gudanar da bikin “Ranar Kauyawa” a faɗin jihar baki ɗaya.

Hukumar tace fina-finan ta bayyana cewa wannan mataki yana cikin ƙoƙarin kare tarbiyyar al’umma, kiyaye al’ada, da kuma tabbatar da daidaiton zamantakewa a jihar.

An haramta Kauyawa a Kano
Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta bikin Kauyawa Hoto: Abba El-Mustapha
Asali: Facebook

Hadimin Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami'in yaɗa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haramta bikin ranar kauyawa a Kano

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Asabar.

Ya bayyana cewa yadda ake gudanar da Ranar Kauyawa a halin yanzu bai dace da ƙa’idojin tarbiyya da addini da mutanen jihar ke tinkaho da su ba.

“Muna ɗaukar wannan mataki ne domin kare darajar al’umma da kuma inganta zaman lafiya a fadin jihar."
"Yadda ake gudanar da Ranar Kauyawa a yau, da shiga ta rashin kamun kai, rawar batsa, da kuma yaɗa abubuwan da ba su dace ba, na barazana ga tarbiyyar al’umma."
"Saboda haka, an haramtawa dukkan wuraren bukukuwa da ɗakunan taro yin kowanne irin taron da ya shafi Ranar Kauyawa har sai an sake duba dokokin da suka shafi irin wannan taro."

- Abba El-Mustapha

Abba El-Mustapha ya ƙara da cewa hukumar za ta haɗa kai da hukumomin tsaro domin tabbatar da bin wannan doka.

“Bayan sanya dokar, muna kuma tattaunawa da shugabannin al’umma, dattawa, ƙungiyoyin matasa da malamai, domin wayar da kai game da illolin wannan biki da kuma samun goyon bayan jama’a kan wannan doka."

- Abba El-Mustapha

Hukuma ta haramta bikin Kauyawa a Kano
An haramta bikin ranar Kauyawa a Kano Hoto: Legit.ng
Asali: Original

An buƙaci malamai su ba da haɗin kai

Hukumar ta kuma buƙaci malamai da malaman addini da su taka rawar gani wajen wayar da kan jama'a.

“Muna kira ga limamai da malaman addini da su yi amfani da mimbarorinsu wajen ilmantar da iyaye da al’umma kan muhimmancin wannan doka.”

- Abba El-Mustapha

Shugaban hukumar ya kuma ce an bukaci hakimai, dagatai da sarakunan gargajiya da su taimaka wajen tabbatar da bin wannan doka.

Abba El-Mustapha ya ja kunnen cewa za a dauki mataki mai tsauri kan duk wani mutum ko ƙungiya da suka karya wannan doka.

Hukumar tace fina-finai ta dakatar da jaruma

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da jarumar Kannywood, Samha M Inuwa.

Hukumar ta dakatar da jarumar ne na tsawon shekara ɗaya bisa zargin sanya tufafin da ba su dace ba da yaɗa bidiyoyin rashin tarbiyya.

Hukumar ta ce fina-finan ta ɗauki matakin ne kan jarumar bayan ƙorafe-ƙorafen da mutane suka shigar a kanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng