Amurka Ta Shiga Maganar Tsare Nnamdi Kanu a Najeriya
- Majalisar Dokokin Amurka ta nemi ministan harkokin wajen ƙasar da ya tattauna da gwamnatin Najeriya kan batun jagoran 'yan aware, Nnamdi Kanu
- Abubuwan da aka so kasashen biyu su tattauna sun hada da batun shari’a, hukunci da kuma tsare shugaban ƙungiyar IPOB din da aka yi a Najeriya
- Matakin ya biyo bayan ƙudurin da majalisar dokokin Amurka ta amince da shi a ranar 22 ga Mayu, 2026 bayan wani zama na musamman da ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Majalisar dokokin Amurka ta umarci ministan jarkokin wajen ƙasar, Marco Rubio da ya tattauna da gwamnatin Najeriya game da shari’a, hukunci da kuma ɗaurin kurkukun shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Gwamnatin Najeriya ta daure Nnamdi Kanu a kurkuku ne bayan samun shi da laifin ta'addancin da ya jawo mutuwar mutane da dama.

Source: Twitter
Umarni ya biyo bayan wani ƙuduri da majalisar ta zartar a ranar 22 ga Mayu, 2026, wanda jaridar Daily Sun ta samu kwafinsa a Abuja a ranar Talata.
Kudirin Amurka kan Kanu
Rahotanni sun nuna cewa kudurin mai lamba H.Res. 1321 ya fito ne daga ɗan majalisar dokokin Amurka, John James.
Ya bukaci majalisar ta matsa wa gwamnatin Najeriya lamba domin tabbatar da cewa duk wata shari’a da ta shafi Kanu ana gudanar da ita ne bisa cikakken bin kundin tsarin mulki da kuma ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam.
An yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai-da-rai a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin mai shari’a James Omotosho.
Karin bayanin Amurka kan Kanu
Baya ga kiran a bi kundin tsarin mulki da ƙa’idojin kare haƙƙin ɗan Adam, dan majalisar Amurka ya bukaci gwamnatin Najeriya ta yi la’akari da rahoton UN WGAD game da tsare Kanu, tare da ɗaukar matakin da ya dace kan shawarwarin da rahoton ya bayar.
Punch ta wallafa cewa wani ɓangare na ƙudurin ya ce a lura da:
“Yin kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa duk wata shari’a da ta shafi Nnamdi Kanu ana gudanar da ita ne cikin cikakken bin tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma alƙawurran ƙasa da ƙasa na kare haƙƙin ɗan Adam.
“Kasancewar Nnamdi Kanu fitaccen ɗan siyasa ne da aka sani da fafutukar kare muradun al’ummomin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya;
“Kasancewar Nnamdi Kanu ya bayyana ra’ayoyinsa kan ‘yancin kai na siyasa da tsarin mulki ta hanyar jawabai da fafutuka;
“Kasancewar an nuna damuwa kan yadda aka kama Nnamdi Kanu a Nairobi, Kenya, a watan Yunin 2021, da kuma yadda aka mayar da shi Najeriya,"

Source: Getty Images
Amurka bata son raba Najeriya
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan majalisar Amurka da ya yawaita magana kan zargin kashe Kiristoci ya magantu kan raba Najeriya.
Riley Moore ya bayyana cewa bai zo Najeriya a kwanakin baya da niyyar neman raba kasar da ta shafe shekara da shekaru a hade ba.
Ya bayyana cewa idan aka raba Najeriya, a bisa hasashen da ya yi, Kiristoci za su sha wahalar da ta wuce kima, musamman a Arewa.
Asali: Legit.ng

