Ranar Dimokuradiyya: Tinubu zai Nuna Ayyukan da Ya Yi a Shekara 3
- Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Tinubu ta kaddamar da kwamitin tsara bikin ranar Dimokuraɗiyya na shekarar 2026
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya sanar da cewa shugaba Bola Tinubu zai yi bayani na musamman a ranar
- Akume ya kara da cewa ranar za ta kasance ta musamman wajen baje kolin nasarorin da gwamnatin Bola Tinubu ta samu a shekara uku
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta ce bikin Ranar Dimokuraɗiyya na bana zai ba da damar nuna nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta samu.
Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin ƙaddamar da Kwamitin Tsara Bikin Ranar Dimokuraɗiyya ta 27 a Abuja.

Source: Facebook
Za a nuna nasarorin Bola Tinubu
Daily Trust ta wallafa cewa Akume ya ce bikin ranar 12 ga Yunin 2026 zai ba gwamnati damar nuna wa ’yan Najeriya irin ribar da aka samu wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, aiwatar da gyare-gyare da sake daidaita ƙasa duk da ƙalubalen da ake fuskanta.
Ya ce Ranar Dimokuraɗiyya wata dama ce ga gwamnati ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da kare manufofin dimokuraɗiyya, ƙarfafa cibiyoyi da kuma tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.
Ya kuma yi bayani kan karrama jaruman gwagwarmayar ranar 12 ga Yuni, 1993, musamman marigayi Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola.
Za a karrama Abiola ne saboda sadaukarwarsa ta taka muhimmiyar rawa wajen amincewa da ranar 12 ga Yuni a matsayin ranar dimokuraɗiyyar Najeriya.
Bunkasar dimokuraɗiyyar Najeriya
Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya bayyana cewa cibiyoyin dimokuraɗiyyar ƙasar sun samu ne sakamakon sadaukarwar ’yan kishin ƙasa da suka yi gwagwarmaya domin tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya.
Ya ƙara da cewa bikin da ake yi a duk shekara wata hanya ce ta girmama tarihinsu tare da tantance irin ci gaban da ƙasar ta samu a fannin dimokuraɗiyya.
Bugu da kari, Punch ta wallafa cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi a majalisar kasa domin isar da wasu sakonni masu muhimmanci.

Source: Facebook
Sauran ayyukan da aka tsara domin bikin sun haɗa da taron manema labarai na duniya a ranar 4 ga Yuni, addu’ar Juma’a ta musamman a ranar 5 ga Yuni, taron ibadar coci na mabiya ɗariku daban-daban a ranar 7 ga Yuni.
Za a yi laccar Ranar Dimokuraɗiyya a ranar 9 ga Yuni, shirye-shiryen da suka shafi matasa da mata a ranar 10 ga Yuni, jawabin shugaban ƙasa ga al’umma a ranar 12 ga Yuni, da kuma liyafar daren bikin Ranar Dimokuraɗiyya.
Fayose ya ce za a bata Tinubu
A wani rahoto, kun ji cewa tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose ya zargi Gwamna Seyi Makinde da neman bata shugaban kasa Bola Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa Ayo Fayose ya ce yana zargin cewa an shirya sace dalibai da malamai a jihar Oyo ne domin bata shugaban kasa.
A zargin da ya yi, Fayose ya ce Gwamna Makinde bai yi abin da ya kamata ba a lokacin da aka sace dalibai da malamansu a makaranta.
Asali: Legit.ng

