Yadda Mata Suka Karbi Haramta Bikin 'Kauyawa Day' a Jihar Kano

Yadda Mata Suka Karbi Haramta Bikin 'Kauyawa Day' a Jihar Kano

Kimanin mako daya ke nan da gwamnatin Kano ta haramta gudanar da bikin 'Kauyawa Day' da wasu daga cikin 'yan matan jihar ke shirya yayin murnar aure.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – A ranar 17 ga watan Mayu, 2025, hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, a ƙarƙashin jagorancin Abba El-Mustapha, ta sanar da cewa ba a amince a sake gudanar da bikin 'Kauyawa Day' a jihar ba.

Daga cikin dalilan da hukumar ta bayar na hana bikin har abada akwai rashin tarbiyya da wasu 'yan mata ke nunawa da kuma shiga da ba ta dace da addini ba a yayin bikin.

Kauyawa/Abba El-Mustapha
Mata sun ba da shawara kan soke 'Kauyawa Day' Hoto: Amb Usman Aminu
Asali: Facebook

Wasu matasa sun nuna rashin jin daɗi kan haramcin da aka sanya, kamar yadda wani tsohon hadimin gwamnatin Kano, Hassan Cikinza Rano, ya bayyana a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ra'ayin wata uwa kan haramta 'Kauyawa day'

Wasu mata mazauna Kano sun bayyana ra’ayoyi mabambanta kan yadda aka soke ranar, wacce da dama ke kallon wata dama ce ta nishadi da walwala.

Wata uwa da ta zanta da Legit Hausa, Malama Maryam, ta ce:

“Gaskiya, a matsayina na uwa, ba zan so a daina bikin ba, saboda ya zama wani bangare na al’ada. Yara dai su daina shigar banza. A sa kaya irin na tsofaffi, kamar dinkin buba, a daura zani, a sa magarya da kurna."
"Wadannan abubuwa ne masu kyau tunda al’ada ce. Shigar da ke bayyana tsiraici ce kadai ba ta dace ba.”

Ta shawarci gwamnati da ta sake duba hukuncin, tare da ware hanya mai ma’ana da za a daidaita yadda 'yan mata da sauran mahalarta bikin za su rika yin shiga domin taya amarya murna a cikin ladabi.

Ra’ayin matan Kano kan hana 'Kauyawa day'

Wasu 'yan mata sun bayyana cewa za su ci gaba da gudanar da bikin kauyawa idan lokacin aurensu ya yi, sai dai ba za su bi tsarin da ake yi yanzu ba.

Hajara, wata budurwa mazauniyar Kano, ta shaida wa jaridar Legit Hausa cewa:

“A matsayina na wacce ba a taɓa yi wa aure ba, idan za a yi aurena, za a yi Kauyawa day. Amma ba irin wacce ake sa T-shirt ba. Zani daban, riga daban. Tun da nishadi ne da kuma al’ada.”
Kauyawa
Gwamnatin Kano ta hana 'Kauyawa day' saboda inganta tarbiyya Hoto: Abba El-Mustapha
Asali: Facebook

Sai dai wata baiwar Allah da ita ma aka kira Maryam ta ce babu wata illa ga bikin:

“Ko yau zan yi aure sai na yi Kauyawa, saboda nishadi ne na rana ɗaya. Babu wanda zai hana mu. Shigar da wasu ke ganin ba ta dace ba, ai ba matsala ba ce. Kawai a hana mu nishadi ake so. Kuma wallahi ba fashi, sai mun yi.”

Yadda aka hana 'kauyawa day' a Kano

A baya, mun wallafa cewa hukumar tace fina-finai da dab’i ta Kano ta sanar da dakatar da dukkannin cibiyoyin shirya bukukuwa a fadin jihar har zuwa wani lokaci a nan gaba.

Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ne ya fadi haka a sanarwar da ya fitar bayan wani taron gudanarwa na hukumar a Kano, inda ya ce an dauki matakin ne saboda kare mutuncin jama'a.

Hukumar ta bukaci hadin kai daga shugabannin al’umma da hukumomin tsaro kamar Hisbah, Kungiyar sai kai ta bijilanti, da masu tsaron unguwanni don tabbatar da bin wannan doka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.