Dattawan Kwara Sun Yi Barazana da 2027 bayan Kashe Masu Mutum 1200 a Mulkin Tinubu

Dattawan Kwara Sun Yi Barazana da 2027 bayan Kashe Masu Mutum 1200 a Mulkin Tinubu

  • Wasu dattawa da masu ruwa da tsaki daga yankin Kwara ta Arewa sun ce jama'a da dama sun rasa rayukansu a hare-haren 'yan bindiga tun bayan hawan mulkin Bola Tinubu
  • Sun bayyana cewa matsalar tsaro ta jefa al'umma cikin firgici, ta lalata tattalin arziki tare da hana manoma zuwa gonakinsu ballantana a samu damar noma abinci
  • Kungiyar ta gargadi jam'iyya mai mulki ta APC a kan sake samun goyon bayan jama'a wajen sake hawa mulki idan aka ci gaba da yi wa rayukan bayin Allah dauki dai-dai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Ilorin, jihar Kwara - Gamayyar dattawa da masu ruwa da tsaki daga yankin Kwara ta Arewa sun nuna matukar damuwa kan yadda matsalar tsaro ke kara ta'azzara a yankin.

Kara karanta wannan

"Za a iya gano su"; Buratai ya dauko batun 'yan bindigan da ke fitowa a bidiyoyi

Kungiyar da ke karkashin Kwamitin Raya Kwara ta Arewa (KNDC) ta yi zargin cewa sama da mutum 1,200 sun mutu sakamakon hare-haren 'yan bindiga da masu aikata ta'addanci tun bayan da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karbi mulki a shekarar 2023.

Mutanen Kwara sun yi kuka da kamun ludayin gwamnati kan rashin tsaro
Shugaban kasa Bola Tinubu a wani taro da aka yi a kasar waje Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa a wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Manzuma, da sakatariyar yada labarai, Hajiya Zainab Seko, suka sanya wa hannu, sun bayyana halin da yankin ke ciki a matsayin kusan rugujewar tsaro gaba daya.

Mutanen Kwara suna kuka da rashin tsaro

Kungiyar ta ce yankin da aka fi sani da kasancewa cibiyar samar da abinci a jihar Kwara ya zama tamkar kufai saboda yawaitar hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai.

A ruwayar jaridar Punch, kungiyar ta bayyana cewa matsalar ta shafi kananan hukumomi biyar da suka hada da Baruten, Kaiama, Edu, Patigi da Moro, inda ta tilasta wa mutane da dama barin gidajensu tare da dakile harkokin tattalin arziki.

Sun ce:

"Mutanenmu suna rayuwa cikin tsoro. An kori al'ummomi gaba daya daga matsugunansu. Sama da rayuka 1,200 sun salwanta, yayin da har yanzu ake rike da maza, mata da yara da dama a hannun 'yan ta'adda da 'yan bindiga."

Kara karanta wannan

Minista a Isra'ila na zuga Netanyahu, yana neman a fara yi wa Amurka bore

Rokon mutanen Arewacin Kwara ga Tinubu

Dattawan sun ce noma, wanda shi ne ginshikin rayuwar mutanen yankin, ya fuskanci babban kalubale saboda rashin tsaro.

Sun kara da cewa:

"Tattalin arzikin yankin ya durkushe, kuma noma ya sha mummunar illa. Yanzu amfanin gona yana lalacewa saboda rashin masu saye."
Kungiyar ta yaba da kokarin gwamnatin Kwara
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: AbdulRahman AbdulRazaq
Source: Facebook

Kungiyar ta yaba da kokarin gwamnatin AbdulRahman AbdulRazaq wajen magance matsalar, amma ta jaddada cewa alhakin kare rayuka da dukiyoyi yana hannun Gwamnatin tarayya.

Dattawan sun yi kira ga shugaban kasa da ya tura karin jami'an tsaro da sauran kayan aiki domin dakile hare-haren 'yan ta'adda a yankin, tare da cewa akwai barazanar APC za ta fuskanci matsala a zaben 2027 idan ba a gyara ba.

Gwamna ya magantu kan zaben Tinubu

A baya, mun wallafa cewa Gwamna Sheriff Oborevwori ya bayyana cewa al'ummar jihar Delta za su kada wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kuri'unsu a zaben 2027 domin ci gaba da cin maoiryar ayyukan gwamnati.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin ta'addanci a Sokoto, an kashe masu yawon Sallah

Ya ce Shugaba Tinubu surukin Delta ne saboda alakar da ke tsakanin uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu da jihar, kuma rashin goyon bayansa zai iya zama wani babban zunubi a babban zaben da ke tafe.

Gwamnan ya kuma yabawa Oluremi Tinubu kan rawar da take takawa wajen karfafa dangantaka tsakanin gwamnatin tarayya da jihar Delta, tare da nanata cewa a yanzu, mai gidanta ne kadai mai alakar kai tsaye da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng