Ba Sani ba Sabo: Gwamnatin Kano Ta Gaji, An Fara Ɗaukan Mataki a kan 'Yan Daba

Ba Sani ba Sabo: Gwamnatin Kano Ta Gaji, An Fara Ɗaukan Mataki a kan 'Yan Daba

  • Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa za ta tsaurara mataki kan masu aikata daba da amfani da makamai wajen tayar da zaune tsaye a fadin jihar
  • Ma’aikatar shari’a ta bayyana cewa za a gaggauta bincike da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a rikice-rikicen daba a gaban kotu nan gaba kadan
  • An kuma bukaci mazauna unguwanni su hada kai da jami’an tsaro domin dakile matsalar da ke kara yaduwa inda matasa ke barazana ga rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bayyana kudirinta na kawo karshen matsalar daba da ta’addancin matasa da ke haddasa tashin hankali a sassa daban-daban na jihar.

Babban Lauyan Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude, ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen hukunta duk wanda aka kama da hannu cikin ayyukan daba ko kuma masu ba su goyon baya.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Cutar kwalara ta kama mutane sama da 4,000 a Borno, an rasa rayuka

Gwamnatin Kano ta dauki mataki a kan fadan daba
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yuauf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

A hira da ya ya yi da kafar BBC Hausa, ya ce karuwar rikice-rikicen daba a wasu yankunan Kano ya sa gwamnati ta dauki sababbin matakai domin dakile matsalar kafin ta kara kamari.

Gwamnatin Kano ta waiwayi matsalar daba

Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru Maude ya bayyana cewa ma’aikatar shari’a na da nata masu binciken da ke aiki tare da hukumomin tsaro wajen tattara hujjoji kan wadanda ake zargi da aikata laifuffuka.

Maude ya ce duk lokacin da bincike ya tabbatar da akwai hujjoji a kan wani mutum, gwamnati za ta tabbatar an gurfanar da shi a gaban kotu domin ya fuskanci hukuncin da doka ta tanada.

Ya jaddada cewa gwamnati za ta yi aiki kafada da kafada da jami’an tsaro wajen tabbatar da cewa masu tada zaune tsaye ba su ci gaba da barazana ga zaman lafiyar al’umma ba.

Gwamnatin Kano ta nemi hadin kan al’umma

Kwamishinan ya kuma bayyana cewa yaki da daba ba aikin jami’an tsaro kadai ba ne, yana bukatar hadin kan gwamnati da al’umma baki daya.

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargi da sace dalibai 300 a Neja

A cewarsa, samun bayanan sirri daga mazauna unguwanni na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen gano maboyar masu aikata laifuka da kuma cafke su cikin sauri.

Ya ce ya zama dole jama’a su kawar da tsoro tare da sanar da hukumomin tsaro duk wani bayani da zai taimaka wajen dakile ayyukan daba a yankunansu.

Gwamnatin Kano ta nemi a hada kai da jami'an tsaro kan matsalar daba
Kwamishinan yan sandan Kano Ibrahim Adamu Bakori a hira da manema labarai a jihar Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

A zantawarta da Legit, wata mazauniyar Kawo a Jjihar Kano, Fatima ta bayana cewa ko daren Larabar nan yan daba sun kawo harin ramuwar gaya unguwar.

Ta ce:

"Sun rika fasa tebura da cire alamun da aka sanya a kan titunanmu wurin 11.00 na dare suka zo, suka gama abinsu suka tafi wurin 11.40 na daren."

Ta ce ita yanzu addu'a take Allah Ya ba su ikon barin unguwar, domin tun kafin Sallah babba ake fadan daba tsakanin unguwannin da ke makwabtaka da juna, wato Kawon Lambu da Kawon Majalisa.

An kashe uban daba a Kano

A baya, kun samu labarin cewa rikicin 'yan daba a Kano ya yi sanadiyyar mutuwar wani uban daba bayan an labta masa sara a wuya yayin wani harin daukar fansa tsakanin matasan Kawo da na Mariri a jihar.

Kara karanta wannan

"Ina tsaro a Kano?" Aminu Gwarzo ya dura a kan gwamantin Abba

Jami'an yan sanda sun yi nasarar kama mutane tara tare da tarwatsa wasu 'yan daba da suka yi kokarin sake tada yamutsi a Mariri, tare da tabbatar da cewa al'amura sun lafa a yankin Kawo a karamar hukumar Nassarawa.

Rahoton ya nuna cewa fadan ya kaure ne tsakanin ƙungiyar uban daba Kabalo Snu da kuma ƙungiyar uban daba Faizu Mohammed, wanda aka fi sani da "Chabross" na Yar Kasuwa, a yankin Kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng