Bayan Sukar APC, ADC da NDC, Babachir Ya Fadi Wanda Zai Zaba a 2027
- Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya caccaki APC, PDP, ADC da NDC, yana cewa dukkan manyan jam’iyyun ba su ba da manufa
- Ya ce zai iya zaɓar matashin ɗan takara a 2027, amma ya bayyana rashin gamsuwa da dukkan manyan ‘yan takarar da ake da su yanzu a Najeriya
- Babachir wanda Muhammadu Buhari ya kora daga ofis ya ce ya yi murabus daga ADC saboda zargin rashin gaskiya a zaben fitar da gwani da aka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal ya caccaki tsarin jam'iyyun APC, PDP, ADC da NDC.
Babachir David Lawal ya ce yana iya zaben matashin dan takarar shugaban kasa a 2027 kan sauran azzaluman jam'iyyu.

Source: Facebook
Babachir ya bayyana hakan a hirarsa da gidan talabijin na TVC bayan ya yi murabus daga ADC saboda zargin rashin daidaito a zaben fitar da gwani.
Wanda Babachir Lawal zai zaba a zaben 2027
Babachir Lawal ya ce yana iya yin la’akari da jefa kuri’a ga 'dan gwagwarmaya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a AAC, Omoyele Sowore, a zaɓen 2027.
A cewarsa:
“Ina da kuri’a guda ɗaya ta kaina idan lokacin ya yi. Ko ma zan iya zaɓar Sowore; akwai wasu ‘yan takara masu tasowa da na yi imanin za su iya tafiyar da Najeriya da kyau.”
Babachir ya ce sukar Tinubu da Atiku ba yana nufin yana goyon bayan wani dan takara ba a zaben 2027.
Ya kuma bayyana cewa ya yi ritaya daga siyasa kuma ba ya yakin neman zabe ga kowa a halin yanzu gaba daya a Najeriya.

Source: Facebook
Babachir ya magantu kan tikitin Obi, Kwankwaso
Da aka tambaye shi ko yana ganin tikitin Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a matsayin zaɓi mai kyau a 2027, Lawal ya ce bai gamsu da manyan zaɓukan siyasa da ake da su a yanzu ba.
Ya ce:
"Na tsinci kaina tsakanin shaidan da shaidan; ɗaya gefen ma shaidan ne. Duk abin da na zaɓa, a ƙarshe shaidan zan samu. Ma'ana, duk yadda Bola Tinubu yake da matsaloli a yanzu, Atiku zai fi shi muni idan ya zama shugaban ƙasa."
Ya ce zai yi amfani da ‘yancinsa na kada kuri’a lokacin zabe, amma har yanzu bai zabi dan takara ba, ya ce ya riga ya ware wasu jam’iyyun siyasa da ba za su samu goyon bayansa a zaben 2027 ba.
Babachir ya zargi Tinubu da iya murde zabe
Mun ba ku labarin cewa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya yi zargin cewa zai yi wuya a kayar da Bola Tinubu a 2027 idan maguɗin zaɓe ne ke tabbatar da nasara.
Babachir ya ce Tinubu zai fi kowane ɗan takara iya murɗe sakamakon zaɓe jim kadan bayan ya sanar da ficewa daga jam'iyyar ADC.
Ya kuma soki Atiku Abubakar tare da bayyana dalilin da ya sa yake kiransa da lakabin “Kachalla” yayin da ya raba gari da tafiyarsu gabanin zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

