Kano: Abba Kabir Ya Ba Masu Shirya Fina Finai Sabon Umarni Domin Yaki da Rashin Tarbiyya

Kano: Abba Kabir Ya Ba Masu Shirya Fina Finai Sabon Umarni Domin Yaki da Rashin Tarbiyya

  • Yayin da ake fama da rashin tarbiyya a jihar Kano, gwamnatin jihar ta dauki mataki kan masu shiryar fina-finai a jihar
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haramta shirya duk wani wasan kwaikwayo da ke ɗauke da 'yan daba ko kuma 'yan daudu
  • Hakan bai rasa nasaba da yawan dabanci da ake samu a birnin Kano wanda ya jawo rasa rayuka da dama a kwanakin nan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kafa sabuwar doka ga masu shirya fina-finai a fadin jihar baki daya.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haramta shirya fim da ke nuna dabanci ko kuma harkar 'yan daudu a jihar.

Kara karanta wannan

Ana cikin azumi mutane sun fasa rumbun ajiya da dasa wawa kan kayan abinci a Arewa

Abba Kabir ya dauki mataki kan masu shirya fina-finai
Abba Kabir haramta shirya fim da ke ɗauke da 'yan daudu da 'yan daba a Kano. Hoto: @abbaelmustapha1.
Asali: Twitter

Yadda 'yan daba suka addabi Kano

Wannan mataki bai rasa nasaba da yawan ta'addanci da ake samu a tsakanin matasa a birnin Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A 'yan kwanakin nan an samu rasa rayuka da dama sanadin ayyukan 'yan daba a birnin Kano da kewaye.

Har ila yau, a Kano ana yawan samun 'yan daudu da ke kawo cikas musamman a kokarin hukumar Hisbah na gyara tarbiyya.

Abin da El-Mustapha ya ce kan matakin

Har ila yau, shugaban Hukumar tace fina-finai a Kano, Abba El-Mustapha ya tabbatar da daukar matakin a shafinsa na Facebook.

El-Mustapha ya ce sun dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen da al'umma ke yi kan shirya fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar daudu a jihar Kano.

Abba El-mustapha ya bada wannan umarni ne jim kadan bayan ganawa da ya yi da manyan ma'aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano

Kara karanta wannan

APC ta dauki zafi kan sharrin da aka yi wa Matawalle, ta gargadi PDP a Zamfara

An haramta bude gidajen gala a Kano

A baya, mun ruwaito muku cewa Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta umarci rufe dukkan gidajen gala a fadin jihar.

Shugaban hukumar a jihar, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 10 ga watan Maris a shafinsa na Facebook.

El-Mustapha ya ce an dauki wannan matakin ne saboda shirye-shiryen da ake yi na tunkarar watan azumin Ramadan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel