Sowore zai Nufi Gidan da Tinubu ke Zaune da Zanga Zanga Mai Zafi

Sowore zai Nufi Gidan da Tinubu ke Zaune da Zanga Zanga Mai Zafi

  • Dan gwagwarmaya a Najeriya, Omoyele Sowore ya fara shirin gudanar da zanga-zanga zuwa fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Sowore ya bayyana cewa ba za su zuba ido suna gani ana sace dalibai da jama'ar kasa ba tare da ana daukar matakin da ya dace ba
  • Ya yi magana ne a Abuja ranar Talata yayin da kungiyar malaman Najeriya (NUT) ta shirya zanga-zanga bayan sace dalibai a Oyo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya shiga zanga-zangar da mazauna Abuja da malamai ke yi domin neman a sako ɗaliban da aka sace a Jihar Oyo.

A cikin wani bidiyo da ya bazu sosai, Sowore ya haɗu da masu zanga-zanga a Babban Birnin Tarayya (Abuja), a nan ya dauki alƙawarin ci gaba da mara masu baya.

Kara karanta wannan

'Tinubu jan wuya ne a murde zabe': Babachir Lawal na ganin APC za ta zarce

Dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore
Omoyele Sowore yayin hira da manema labarai. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Sowore ya ce shi ma yana shirin gudanar da zanga-zangar shi zuwa Fadar shugaban kasa.

Yele Sowore ya caccaki gwamnatin Tinubu

Yayin zanga-zangar, ɗan gwagwarmayar ya soki Shugaban ƙasa kan gazawa wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

“Ba mu roƙon kowa. Abin da muke nema kawai shi ne waɗanda suke cewa an zaɓe su domin kare jama’a su yi aikinsu,”

In ji Sowore.

“Da zai fi kyau idan adadin ‘yan sandan da ake amfani da su wajen hana wannan zanga-zanga ana amfani da su wajen kare makarantu.
‘Ya’yanku ma suna makarantu. Idan makarantu suka zama wuraren sace mutane, wata rana za a iya sace ‘ya’yanku. Ina fatan hakan ba zai faru ba.
“Lokaci ne da ya kamata kowa ya haɗa kai, ya yi amfani da hankali kuma ya aikata abin da ya dace. Nan gaba kaɗan za a ga ƙarin irin wadannan zanga-zanga. Wannan farkon lamarin ne kawai. Ba za mu ja da baya ba."

Kara karanta wannan

Ana zargin gwamna Oyo da shirya sace dalibai don bata sunan Tinubu

Omoyele Sowore a wajen zanga-zanga
Omoyele Sowore tare da 'yan NUT masu zanga-zanga a Abuja. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Facebook

Zanga-zangar da Sowore ya shirya

Omoyele Sowore ya bayyana cewa a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni zai jagoranci gangami zuwa fadar shugaban kasa a Abuja.

“Ranar Alhamis za mu tafi Aso Rock Villa idan ba a ceto yaran ba. Ba za ka iya cewa kai ne shugaban Najeriya sannan ka ƙi yin aikin babban kwamandan rundunar sojoji ba.”

Ya bayyana cewa matasa da zai jagoranta a lokacin zanga-zangar za su hadu ne a filin taro na Eagle Square da ke Abuja.

Ga bayanin Sowore da NewsCentral TV ta wallafa a X:

Jama'a sun yi zanga-zanga a Oyo

A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Take It Back ta gudanar da zanga-zangar adawa da sace dalibai a jihar Oyo ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa sun fara zanga-zangar ne domin neman a gaggauta ceto ɗalibai da malaman da aka sace a watan da ya wuce.

A lokacin harin, 'yan ta'addan sun kashe mataimakin shugaban makarantar da kuma wani matukin babur kafin su tafi da ɗaliban.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng