'Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Rikita Lissafin APC, Sun Sauya Sheka zuwa ADC da PRP

'Yan Majalisar Tarayya 3 Sun Rikita Lissafin APC, Sun Sauya Sheka zuwa ADC da PRP

  • 'Yan majalisar wakilai ta tarayya uku sun sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyyun adawa na PRP da ADC gabanin zaben 2027
  • Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ne ya karanta takardun sauya shekar tasu a zauren majalisa yau Laraba, 3 ga Yuni, 2026
  • Wannan na zuwa ne bayan kusan duka jam'iyyun siyasa sun kammala zabukan fitar da 'yan takararsu na babban zabe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jam'iyyar APC ta sake fuskantar koma baya bayan wasu mambobi uku na majalisar wakilai sun mika takardar ficewa daga jam'iyya mai mulki.

'Yan Majalisar wakilan sun sanar da sauya shekarsu daga APC zuwa jam'iyyun adawa PRP da ADC a hukumance yau Laraba, 3 ga watan Yuni, 2026.

Majalisa.
Yan Majalisar wakilai yayin da suke tsakiyar zama a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ne ya sanar da sauya shekar 'yan majalisar yayin zaman majalisar da aka gudanar ranar Laraba, kamar yadda The Cable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan ficewar Babachir, sabuwar rigima ta bullo a ADC a jihar Adamawa

Yan Majalisar da suka fice daga APC

Daga cikin 'yan majalisar da suka bar APC akwai Hon. Rabilu Bala, mai wakiltar mazabar Jama'are/Itas-Gadau ta jihar Bauchi, wanda ya koma jam'iyyar PRP.

Sauran biyu sun hada da Hon. Abubakar Zango, mai wakiltar mazabar Yola ta Arewa/Yola ta Kudu/Gire a jihar Adamawa, da kuma Hon. Abdullahi El-Rasheed, mai wakiltar mazabar Dukku/Nafada ta jihar Gombe.

Duka wadannan 'yan Majalisa guda biyu sun sanar da sun ficewa daga APC tare da komawa jam'iyyar ADC, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

Sauya sheka na karuwa gabanin 2027

Majalisar wakilai na ci gaba da fuskantar sauye-sauyen siyasa tun farkon shekarar nan, yayin da jam'iyyu ke kokarin karfafa matsayinsu kafin babban zaben shekarar 2027.

A ranar Talata da ta gabata, 'yan majalisar wakilai takwas sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar adawa ta APM.

Haka kuma, wasu 'yan majalisa uku sun sauya sheka daga APC zuwa PDP da kuma NDC.

Kara karanta wannan

2027: NDC ta jawo tsohon shugaban matasan APC, ta tsaida shi takarar gwamna a Gombe

Majalisa.
Yadda yan Majalisa ke zama a zauren Majalisar wakilai ta kasa da ke Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Masu sharhi kan harkokin siyasa na ganin irin wadannan sauye-sauyen sheka na nuna yadda siyasar Najeriya ke kara daukar sabon salo yayin da manyan jam'iyyu ke kokarin jawo manyan 'yan siyasa zuwa cikinsu.

Ana sa ran za a ci gaba da ganin irin wadannan sauye-sauye a watanni masu zuwa, musamman bayan kammala zabukan fidda gwani da jam'iyyu ke gudanarwa domin shirye-shiryen zaben 2027.

Hon. Chinda ya ajiye mukaminsa a majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa dan takarar gwamnan jihar Rivers na jam'iyyar APC, Hon. Kingsley Chinda ya ajiye mukamin Shugaban marasa rinjaye na Majalisar wakilai.

Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ne ya sanar da murabus, in da ya sanar da cewa Hon. Chinda ya sauya shekar daga PDP xuwa APC.

Chinda ya kuma tabbatar da cewa duk da murabus dinsa daga mukamin jagoran marasa rinjaye, zai ci gaba da gudanar da aikinsa a matsayin dan majalisa tare da mara wa ayyukan majalisar baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262