Ana neman daraktan fim din Kannywood ruwa a jallo bisa shirya fim din koyar da jima'i

Ana neman daraktan fim din Kannywood ruwa a jallo bisa shirya fim din koyar da jima'i

  • Wani mai shirya fina-finan Kannywood ya shiga tarkon hukumar tace fina-finai saboda shirya wani fim da bai yi kyau ba
  • Hukumar tace fina-finai ta ce fim din ya saba da al'adar Hausawa da Kanawa, don haka dole a nemo wanda ya shirya shi
  • Sai dai, wanda ya shirya fim din ya ce shi sam bai aikata wani laifi ba, don haka ba zai amsa gayyatarsu ba

Kano - Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta bayyana cewa tana neman, Aminu Umar Mukhtar, daraktan fina-finan Kannywood, ruwa a jallo akan shirya wani fim mai ‘Makaranta’.

Na Abba Afakallah, babban daraktan hukumar ne ya bayyana haka a zantawarsa da BBC Pidgin ranar Alhamis.

Afakallah ya ce matakin ya biyo bayan rashin girmama gayyatar da hukumar ta yi masa kan fim din, The Cable ta tattaro.

Kara karanta wannan

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

Aminu Muktar, mai shirin Makaranta
Ana neman daraktan fim din Kannywood ruwa a jallo bisa shirya fim mai koyar da jima'i | Hoto: qed.ng
Asali: UGC

A cewarsa, daraktan fim din a watan Disamba ya yi alkawarin bayyana a ofishin tace fina-finan a sabuwar shekara amma har yanzu bai yi hakan ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce rashin amincewar da hukumar ta yi na aikin fim din ya samo asali ne saboda abubuwan da ke ciki ‘na ’ da kuma yadda bai samu amincewar hukumar ba.

A cewarsa:

“Gaskiyar magana ita ce duk tsarin fim din bai samu goyon bayan hukumar ba. Hatta bidiyon talla da ke yawo a halin yanzu ya kamata mu tantance. Ta haka ne za mu iya cewa a cire wannan bangare ko wancan, amma mai shirya fim din bai yi ko daya ba.”
"Tunda bai amsa gayyatar da muka yi masa ba, za mu dauki mataki na gaba saboda hukumarmu na kula da addini da al'adun Kano ne kuma ba za mu bar kowa ya lalata mana hakan ba."

Kara karanta wannan

Shahararren mawaƙin Najeriya, Wizkid, ya ce bai yarda da addini ba

‘Ban yi wani kuskure ba’ – Mukhtar ya mayar da martani

Da yake magana game da batun, Mukhtar ya ce har yanzu bai damu da gayyatar hukumar ba, yana mai jaddada cewa bai yi wani kuskure ba.

Mai shirya fim din ya caccaki gayyatar da aka yi masa, inda ya ce fim dinsa ba na al’ummar Hausawa kadai ba ne, ba a Kano aka yi shi ba.

A kalamansa:

“Lokacin da na ji hukumar tana nemana, ban damu da komai ba, domin ban yi wani kuskure ba.”
“Fim dina ba wai kan Kano ko Hausawa kadai ba ne, kusan harsuna 17 ne aka gabatar a cikin shirin. Haka kuma ban dauki fim din a jihar Kano ba. Don haka, ban fahimci dalilin da ya sa jininsu ya hau a kan batun ba.
“Fim dina ba wai kan ilimin jima’i ne kawai ba, yana dauke da wasu abubuwa kamar kaciyar mata (FGM).

Kara karanta wannan

Sabon salo: Ministan Buhari ya fitar imel dinsa, ya roki 'yan Najeriya su fadi ra'ayinsu akan aikinsa

“Da aikin, muna da burin wayar da kan jama’a game da abubuwan da ke faruwa ba a cikin al’ummar Hausawa kadai ba har ma da sauransu.

A cikin tallan fim din da bai wuce minti uku ba da aka fitar kwanan nan, an ga dalibai a wani yanayi na makaranta.

Daya daga cikin abubuwan da suka faru ya nuna wata daliba tana batu kan ‘Jima’i’.

A wani wurin kuma, an ga wata daliba tana sanar da cewa tana dauke da juna biyu tare da kawarta na mata alkawarin taimaka mata wajen shawo kan lamarin.

Wuri na karshe a cikin tallan ya nuna daliban a cikin wani yanayi na shagali, tare da abokansu maza da mata suna rawa tare.

Gani ya kori ji:

Bayan dogon jira, fim din 'Gidan Badamasi' zango na 4 zai shiga kasuwa nan kusa

A wani labarin, shirin wasan barkwanci na Gidan Badamasi zango na 4, wanda ake jira shine zai zai shigo kasiwa a ranar 6 ga Janairu, 2022, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tuna baya: Buhari ya kasa cika alkawurransa saboda bashi da mukarrabai nagari, Bashir Tofa

Malam Falalu Dorayi, wanda shi ne ya shirya shirin, ya ce zango na 4 zai fi armashi fiye da na baya domin an sake samo sabbin taurari masu barkwanci da karin kwararrun ma’aikata fiye da da.

Falalu ya kuma bayyana cewa an dauki shirin a wurare daban-daban a jihar Kaduna kuma an cusa wasu sabbin sassa masu ban sha'awa a cikin shirin domin kayatar da masu kallo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel