Babban Dalilin da Yasa aka Haramta Bikin 'Kauyawa Day' a Fadin Jihar Kano
- Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da duk wani bikin Kauyawa a jihar da ke Arewa maso Yammacin Najeriya
- Sakatare janar na hukumar, Abba El-Mustapha ya ce matakin yana da nasaba ne da gyaran dokar 2025 da gwamnatin jihar ta rattaba hannu a kai
- An bukaci hadin gwiwa daga shugabannin al’umma da hukumomin tsaro don tabbatar da bin umarnin da hukumar ta fitar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Jihar Kano - Sakatare Janar na Hukumar Tace Fina-Finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya bayyana cewa gwamnati ta dakatar da duk wasu bukukuwa da ake kira Kauyawa Day,
A wata sanarwa da ya fitar bayan taron gudanarwa na hukumar tace fina-finai, y ace, hukumar ta rufe dukkan cibiyoyin shirya bukukuwa har zuwa wani lokaci.
El-Mustapha ya ce wannan mataki na daga cikin kokarin da hukumar ke yi don kare tarbiyya da inganta zaman lafiya a cikin al’umma.

Asali: Facebook
Dalilin dakatar da Kayuawa Day
A cewarsa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Mun dauki wannan mataki ne bisa sabuwar gyaran doka da majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da ita a shekarar 2025, wadda kuma gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sanya hannu a kanta.”
Ya bayyana cewa sabuwar dokar ta bai wa hukumar ikon lura da ayyukan DJs, masu shirya bukukuwa da cibiyoyin taro a fadin jihar.
Kauyawa Day a mahangar dokar Kano
Sakatare Janar din ya kara da cewa, duk wani biki da aka shirya a matsayin Kauyawa Day yanzu ya zama laifi bisa doka, rahoton Daily Trust.
Ya bukaci shugabannin al’umma da hukumomin tsaro kamar Hisbah, Kungiyar Vigilante ta jihar da sauran masu tsaron unguwanni su hada kai da hukumar wajen tabbatar da ganin an bi wannan doka.
Ya kara da cewa:
“A halin yanzu, duk wani biki na Villagers Day (Kauyawa) an haramta shi kuma wanda ya saba doka, ma iyi zai fuskanci hukunci. Muna kira ga duk masu ruwa da tsaki da su bada hadin kai domin ci gaban al’ummarmu.”
Su waye wannan doka ta tanada?
Daga cikin cibiyoyin da hakan zai shafa akwai wuraren da matasa ke shirya bukukuwa, da na haya da ake amfani da su wajen yin shagulgula, kamar gidan bikin aure, coci-coci, da kuma ‘club’.
Wannan matakin dai ya haifar da cece-kuce a tsakanin al’umma, musamman matasa da ke amfani da irin wadannan bukukuwa domin sada zumunta da tunawa da asalinsu na kauye.
Wasu na ganin hakan zai dakile shaye-shaye da fasikanci da ke faruwa a irin wadannan bukukuwa, yayin da wasu ke kallon matakin a matsayin tauye ‘yancin jama’a na walwala.
A halin yanzu, hukumar tace fina-finai ta bayyana cewa za ta ci gaba da sa ido tare da daukar matakan doka ga duk wanda ya saba da wannan sabon tsarin.
Yadda aka kame masu maganin gargajiya
A wani labarin, Shugaban hukumar tace finafinai da ɗab'i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya yi ƙarin haske kan kamen da hukumar ke yi na masu siyar da magungunan gargajiya.
Al-Mustapha ya bayyana cewa hukumar ta fara kamen ne akan masu siyar da magungunan gargajiyan da su ke amfani kalaman batsa wajen gudanar da tallansu.
Shugaban ya kuma bayyana cewa kamen ya shafi hada masu talla waɗanda suke amfani da hotunan rashin ɗa'a da nufin jan hankulan masi siya wajen tallata magungunansu.
Asali: Legit.ng