Iran Ta Amince da Mika Muhimmin Arzikinta domin Yarjejeniya da Amurka
- Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta amince za ta mika tarin sinadarin uranium da aka tace sosai a kasar
- Majiyoyi sun bayyana cewa hakan na da nasaba da yarjejeniyar da aka ce shugaban Amurka Donald Trump ya sanar
- Rahotanni suka ce jami’an Amurka biyu sun tabbatar Iran na da isasshen uranium da zai iya kera bama-baman nukiliya guda 11
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta amince da wani shiri na musamman domin tabbatar da yarjejeniya da Amurka.
Iran ta amince ta mika tarin sinadarin uranium da aka tace sosai a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar da shugaban Amurka, Donald Trump.

Source: Getty Images
Jaridar New York Times ta rawaito cewa jami’an Amurka biyu sun bayyana Iran ta yarda da wata sanarwa da za ta tabbatar da mika uranium ɗin.
Majalisar Amurka ta daga wa Trump kafa
Hakan ya biyo bayan shirin da majalisar Amurka ta yi na tilasta wa Trump bin ka'ida musamman game da yaki da Iran wanda ake ganin zai taimaka wurin dakile yunkurin shugaban Amurka.
Amurkawa da dama na nuna adawa game da matakin Donald Trump musamman yadda yake yakar kasashen duniya madadin mayar da hankali kan matsalolin da kasar ke fama da su.
Jam’iyyar Republican a Majalisar Wakilai ta Amurka ta dakatar da kada kuri’ar takaita ikon yaƙin da Donald Trump yake yi da kasar Iran.
‘Yan Democrat sun zargi shugabannin Republican da kare Trump daga suka, suna cewa kudirin zai samu goyon bayan jam’iyyu biyu idan aka kada kuri’a.
Dan majalisar New York, Gregory Meeks, ya ce an dage zaben ne saboda shugabanni sun fahimci kudirin zai yi nasara cikin sauki a majalisa.

Source: Getty Images
Adadin uranium da Iran za ta sadaukar
Rahoton ya bayyana cewa adadin uranium ɗin da Iran ke da shi zai iya isa a ƙera bama-baman nukiliya guda 11 idan aka yi amfani da shi, cewar Jerusalem Post.
Batun yadda za a kawar da uranium ɗin, wanda Trump ya kira “ƙurar nukiliya,” ya kasance babban abin da ya hana cimma matsaya cikin tattaunawar.
Yayin da Iran ke neman a fayyace makomar tarin uranium ɗinta bayan cimma yarjejeniyar dakatar da yaƙi, jami’an Amurka sun yi barazanar sake kai hare-hare.
Rahoton ya ce jami’an Amurka sun gargadi Iran cewa za su ci gaba da kai hare-hare idan har ta ƙi amincewa da mika sinadarin uranium ɗin domin tabbatar da shirin zaman lafiya.
An yi harbe-harbe kusa da fadar Trump
Mun ba ku labarin cewa wani mutum ya zaro bindiga daga cikin jaka ya yi harbi kan jami'an tsaro a kusa da fadar White House ta kasar Amurka.
Jami'an tsaro sun mayar da martani wanda hakan ya jawo aka yi musayar wuta wadda ta jawo asarar rai da raunata wani mutum.
Hukumomi sun bayyana cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump, yana cikin fadar White House lokacin da lamarin ya auku.
Asali: Legit.ng

