'Yan Sandan Jihohi: Tinubu Ya Aika Bukatar Gyara Kundin Tsarin Mulki ga Majalisa

'Yan Sandan Jihohi: Tinubu Ya Aika Bukatar Gyara Kundin Tsarin Mulki ga Majalisa

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya dauki mataki na gaba domin a tabbatar da an samar da 'yan sandan jihohi a fadin Najeriya
  • Rahotanni sn ce ya aika wa Majalisar Wakilai kudirin gyaran Kundin Tsarin Mulkin 1999 wanda zai yi sharar fage wajen samar da doka kan batun
  • Tinubu ya ce kudirin zai taimaka wajen sake fasalin tsarin tsaron ƙasa tare da ƙara wasu matakan kariya domin tabbatar da tsaron rayuka yadda ya dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci Majalisar Wakilai ta yi wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 kwaskwarima domin ba da damar kafa rundunar 'yan sandan jihohi.

A cikin wasiƙar da ya aika wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, shugaban ƙasar ya miƙa Kudirin Gyaran Kundin Tsarin Mulki na Tarayyar Najeriya (Kafa 'Yan Sandan Jihohi), 2026 domin majalisar ta fara duba shi.

Kara karanta wannan

Yan sandan jihohi: Barau Jibrin ya fadi amfanin shirin ga Arewacin Najeriya

Tinubu ya aika kudirin yan sandan jihohi ga majalisa
Wasu daga cikin yan majalisa a zaurensu, shugaba Bola Tinubu Hoto: House of Representatives/Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Tinubu ya ce kudirin zai samar da tubalin doka da zai ba jihohi damar kafa rundunar 'yan sandansu.

Dalilin Tinubu na aika kudiri majalisa

Jaridar Leadership ta kawo labarin cewa shugaban ƙasar ya bayyana cewa an ƙara wasu matakan kariya a cikin kudirin domin tabbatar da cewa tsarin 'yan sanda biyu zai fara aiki cikin sauri da kuma yadda ya kamata domin amfanin 'yan Najeriya.

Tinubu ya ce amincewa da dokar yan sandan jihohi zai taimaki Najeriya
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Ya ce:

"Kudirin da aka gabatar muhimmin ɓangare ne na dabarun gwamnatinmu na sake fasalin tsarin tsaron Najeriya domin kare rayuka da dukiyoyin 'yan ƙasa yadda ya kamata."

Shugaba Bola Tinubu ya kuma nuna ƙwarin gwiwar cewa Majalisar Wakilai za ta gaggauta nazari tare da amincewa da kudirin domin jama'a su amfana.

Shugaba Tinubu ya kara kaimi

Rahoton ya ce gwamnatin Tinubu ta sake ƙara ƙaimi wajen neman kafa 'yan sandan jihohi yayin da rashin tsaro ke kara addabar mazauna sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shettima ya kai wa Tinubu ziyara bayan APC ta tabbatar da shi a tikitin 2027

Gwamnoni, masana harkokin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki ke ci gaba da kira da a aiwatar da tsarin domin magance matsalolin rashin tsaro, da suka haɗa da ta'addanci, garkuwa da mutane da rikice-rikicen al'umma.

Idan Majalisar Tarayya ta amince da kudirin, sannan kuma ya samu goyon bayan yawan majalisun dokokin jihohin da kundin tsarin mulki ya tanada, jihohi za su samu cikakken ikon kafa da gudanar da nasu rundunar 'yan sanda.

Gwamnati ta yi magana kan yan sandan jihohi

A baya, mun wallafa cewa Fadar Shugaban Kasa a Najeriya ta yi karin haske game da shirin kafa ƴan sanda a fadin jihohin kasar nan inda ta ce akwai yakinin cewa zai taimaka wajen fuskantar rashin tsaro.

Gwamnatin ta bayyana cewa an samu gagarumin ci gaba wajen kafa ‘yan sandan domin inganta tsaro a kasar, kuma ana jiran masu ruwa da tsaki su amince da dokokin da za a canja domin tabbatar da shi.

An ce tattaunawar kafa ‘yan sandan ta fara watanni da suka gabata bisa umarnin Bola Tinubu, yanzu ya kai matakin gyaran doka, sai dai masana suna kara gargadin a yi duba na tsanaki domin kaucewa matsaloli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng