Iran Ta Rufe Hormuz Gaba Daya, Ta Farmaki Jiragen da Suka Yi Taurin Kai

Iran Ta Rufe Hormuz Gaba Daya, Ta Farmaki Jiragen da Suka Yi Taurin Kai

  • Iran ta sanar da rufe mashigar Hormuz gaba ɗaya ga dukkan jiragen ruwa da ke son wucewa ta hanyar bayan sabon rikcin da ya barke a Gabas ta Tsakiya
  • Biyo bayan lamarin, rundunar sojin ruwan Iran ta kai hari kan wasu jiragen kasuwanci biyu da suka yi ƙoƙarin wucewa ta hanyar da ta ce ta rufe kirif
  • Rahotanni sun nuna cewa an ji ƙarar fashewa a biranen gabar teku na Bandar Abbas da Sirik da kuma tsibirin Qeshm da ke kusa da mashigar Hormuz

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Tashin hankalin da ake tsakanin Amurka da Iran ya dawo sabo kwanaki kaɗan bayan Isra'ila da Iran sun yi musayar hare-hare a mafi muni tun bayan tsagaita wutar da aka cimma a watan Afrilun 2026.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna ya umarci rufe makarantu bayan samun rahoton DSS

Yakin da ya sake barkewa tsakanin kasashe ya jawo kai hare-hare kan wasu muhimman abubuwan more rayuwa a Iran da sansanonin sojin Amurka.

Wasu jirage a hanyar Hormuz
Jiragen ruwa sun nufi hanyar Hormuz kafin a toshe ta. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Iran ta toshe Hormuz kirif

Reuters ta wallafa cewa rundunar sojin Iran ta sanar da rufe mashigar Hormuz a ranar Alhamis ga tankokin mai da jiragen kasuwanci, tana mai cewa duk wani jirgin da ya yi ƙoƙarin wucewa za a harbe shi.

Kafofin yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an kai hari kan wasu jiragen ruwa biyu da suka karya dokar yayin da suke ƙoƙarin wucewa ta Hormuz jim kaɗan bayan Iran ta sanar da rufe wannan muhimmiyar hanyar ruwa bayan hare-haren Amurka.

"Wannan na sake nuna cewa har yanzu yarjejeniyar zaman lafiya tana da rauni, kuma fitar da makamashi daga Tekun Fasha zai ci gaba da fuskantar ƙuntatawa sosai,"

In ji masu nazari na ING a cikin wani bayani ga kwastomominsu.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump a lokacin da zai yi tafiya zuwa China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Farashin mai ya tashi sama

Farashin mai ya yi tashin gwauron zabi a ranar Alhamis bayan Tehran ta ayyana cewa ta rufe mashigar Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi, bayan Amurka ta ƙaddamar da ƙarin hare-hare kan Iran.

Kara karanta wannan

"Za su dandana kudarsu"; Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran bayan musayar hare hare

Farashin danyen man Brent ya ƙaru da dala 1.48, inda ya kai kashi 1.59 cikin 100, zuwa Dala 94.58 kan ganga da misalin ƙarfe 02: 43 na dare.

Danyen man West Texas Intermediate (WTI) na Amurka ya tashi da dala 1.71, inda ya kai kaso 1.90 cikin 100, zuwa dala 91.74.

A yanzu haka dai shugaban Amurka, Donald Trump ya yi alƙawarin ƙarin hare-hare idan ba a cimma yarjejeniyar zaman lafiya da Iran ba.

Iran ta kai hari kan kan Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta kai hare-haren kan Amurka bayan ta zarge ta da maimaita karya yarjejeniyar tsagaita wuta da suka kulla.

Hare-haren sun biyo bayan sanarwar rundunar CENTCOM ta Amurka cewa ta sake kai hare-hare kan wurare da dama a cikin Iran.

Sojojin sun ce an kai hare-haren ne bisa umarnin shugaba Donald Trump kuma a matsayin martani ga abin da suka kira hare-haren Iran marasa dalili.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng