A Karo na 3 a Jere, Amurka Ta Kai Munanan Hare Hare kan Kasar Musulunci Ta Iran

A Karo na 3 a Jere, Amurka Ta Kai Munanan Hare Hare kan Kasar Musulunci Ta Iran

  • Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta kai farmaki kan kasar Musulunci ta Iran a karo na uku cikin kwanaki uku da suka gabata
  • Wannana hari na zuwa ne bayan Shugaba Donald Trump ya ce zai sake kakaba takunkumin hana jiragen ruwa na kasar Iran zirga-zirga
  • A nata bangaren, kasar Iran ta mayar da martani da hare-hare kan wuraren da ke da alaƙa da sojojin Amurka a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Dakarun sojojin kasar Amurka sun sake kai sababbin hare-haren kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a karo na uku cikin kwanaki uku a jere.

Wannan na zuwa ne yayin da Shugaba Donald Trump ya bayyana shirin sake kakaba takunkumin hana jiragen Iran wucewa daga ranar Talata, 14 ga watan Yuli, 2026.

Trump.
Shugaban Amurka, Donld Trump daga bangaren dama da jirgin ruwan sojoji lokacin da suka harba makami Hoto: US Army
Source: Getty Images

Tashar Channels tv ta ruwaito cewa duk da ci gaba da hare-haren, Trump ya ce har yanzu akwai yiwuwar cimma yarjejeniya da Iran.

Kara karanta wannan

Trump ya daina boye boye, ya fadi abin da zai faru idan Amurka ta kwace Hormuz

Sai dai a gefe guda, Iran ta kai hari kan wasu jiragen ruwa biyu a mashigar Hormuz, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani ma'aikacin jirgin, kamar yadda Hadaddiyar Daular Larabawa ta tabbatar.

Amurka ta ce ta lalata ƙarfin Iran

Sojojin Amurka sun bayyana cewa aikin da ya ɗauki sa'o'i biyar ya kai hare-hare kan wurare da dama a Iran, ciki har da Bushehr da Bandar Abbas da ke bakin teku.

A cewarsu, manufar harin ita ce rage ƙarfin Iran na kai hare-hare kan jiragen ruwa na kasuwanci a mashigar Hormuz.

Kasar Iran ta mayar da martani

Bayan hare-haren Amurka, dakarun kare juyin juya halin Iran sun sanar da cewa sun harba makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa zuwa Bahrain.

Sun ce hare-haren sun kai wani ginin zama da sojojin Amurka ke amfani da shi da kuma wasu wurare.

Trump ya shaida wa manema labarai a Fadar White House cewa:

"Za mu kai musu mummunan hari a daren nan, kuma za mu sake kai wani gobe."

Hormuz ta sake zama cibiyar rikici

NBC News ta ce sanarwar Trump kan sake kakaba takunkumi a mashigar Hormuz ta zo ne bayan hare-haren da Amurka da Iran suka kai wa juna, mafi muni tun bayan tsagaita wutar da aka cimma a watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi, ƙasar Iran ta dauki matakin da Amurka ba ta so a Hormuz

Hormuz.
Jiragen dakon kaya na wucewa ta mashigar ruwa ta Hormuz Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Iran ta fara hana zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar bayan hare-haren Amurka da Isra'ila a watan Fabrairu, wanda ya sa Washington ta kakaba takunkumi kan tashoshin jiragen ruwan Iran.

Sai dai an sassauta waɗannan matakai bayan ɓangarorin sun cimma wata yarjejeniya ta farko a watan Yuni.

Farashin danyen mai ya ƙaru da sama da kashi tara cikin 100 ranar Litinin sakamakon fargabar sake ɓarkewar rikici, sannan ya sake ƙaruwa da sama da kashi ɗaya cikin 100 ranar Talata.

Amurka za ta ba jirage tsaro a Hormuz

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta kula da mashigar ruwan Hormuz tare da neman a biya ta kuɗin tsaro da za ta ba jirage.

Trump ya bayyana hakan ne a wata hira ta wayar tarho da aka yi da shi yayin da rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba da ƙamari.

A cewar Trump, Amurka za ta kasance mai kula da mashigar, wadda ke daga cikin muhimman hanyoyin jigilar ɗanyen mai da iskar gas a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262