Matsala Ta Tunkaro ADC da Kotun Daukaka Ta Yanke Hukunci kan Zaben Shugabanni

Matsala Ta Tunkaro ADC da Kotun Daukaka Ta Yanke Hukunci kan Zaben Shugabanni

  • Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin da ya hana INEC amincewa da tarukan zaben shugabannin ADC a jihohi da shugabancin David Mark ya shirya
  • Alƙalai biyu sun goyi bayan hukuncin, yayin da shugaban kwamitin alƙalan ya nuna rashin amincewa da shi
  • Kotun ta ce kwamitocin zartarwa na jihohi ne ke da ikon shirya tarurrukan zaben jam'iyya a a matakin jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta yi hukunci a karar da neman hana hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), amincewa ko halartar tarurrukan zaben shugabanni na jihohi na jam'iyyar ADC.

Kotun daukaka karar ta tabbatar da hukuncin da ya hana hukumar INEC amincewa ko halartar duk wani taron zaɓen shugabanni na jihohi da aka shirya ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark a jam'iyyar ADC.

Kara karanta wannan

Lokaci ya fara ƙurewa, Tinubu ya sanya wa'adin da kowane ɗan Najeriya zai mallaki NIN

Kotu ta yi hukunci a karar ADC
David Mark da Rauf Aregbesola a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: @OfficialADCNg
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta kawo rahoton cewa kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Litinin, 13 ga watan Yulin 2026.

An tabbatar da umarnin da aka ba INEC

A hukuncin da ya jagoranta, Mai Shari'a Okon Abang ya ce kotun ba ta ga wani dalili da zai sa ta soke umarnin da babbar kotun tarayya ta bayar a ranar 29 ga Afirilu kan shugabancin David Mark ba.

Tun da farko, Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ta hana shugabancin ADC da David Mark ke jagoranta tsoma baki cikin wa'adin mulki da ayyukan zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyyar a matakin jihohi.

Kotun ɗaukaka ƙarar ta kuma amince cewa alhakin shiryawa da gudanar da tarurrukan jam'iyya a matakin jiha yana hannun zaɓaɓɓun kwamitocin zartarwa na jihohi, ba shugabancin jam'iyyar na ƙasa ba.

Alƙalai sun rabu kan hukuncin

Yayin da mai shari'a Okon Abang da mai shari'a Donatus Okorowo suka amince da hana INEC karɓar sakamakon zaben da shugabancin David Mark ya gudanar, shugaban kwamitin alƙalan, mai shari'a Abba Mohammed, ya yi sabanin ra'ayi.

Kara karanta wannan

Dalla dalla: Yadda za a kai korafi ga EFCC kan zargin damfara, badakala

A hukuncinsa na rashin rinjaye, mai shari'a Abba Mohammed ya ce shari'ar ta shafi al'amarin cikin gida na jam'iyyar siyasa ne, wanda bai kamata kotu ta shiga cikinsa ba.

Mai Shari'a Abba Mohammed ya ce babbar kotun tarayya ta yi kuskure wajen sauraron ƙarar, tashar Channels tv ta kawo rahoton.

Abin da babbar kotun tarayya ta yanke

A hukuncinta, babbar kotun tarayya ta bayyana cewa wa'adin shekaru huɗu na kwamitocin gudanarwa da kwamitocin zartarwa na ADC a jihohi na ci gaba da aiki har sai an gudanar da sahihan tarurrukan jam'iyya tare da yin babban taro na ƙasa.

Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da wasu mambobin ADC da suka nuna rashin gamsuwa suka shigar a gaban kotun.

Masu ƙarar sun haɗa da Don Norman Obinna, Johnny Tovie Derek, Obah C. Ehigiator, Olona Yinka, Charles Idowu Omideji, Samuel Pam Gyang da Obianyo Patrick.

Sun bayyana cewa sun shigar da ƙarar ne a madadinsu da kuma a madadin dukkan shugabannin jam'iyyar na jihohi da kwamitocin zartarwa na ADC a faɗin ƙasa.

Kara karanta wannan

An kuma samun matsala a shari'ar da aka nemi ƙwace kadarorin Malami a Abuja

Kotun ta yi hukunci a shari'ar ADC
Shugaban jam'iyyar ADC na kasa, Sanata David Mark Hoto: Senator David Mark
Source: Twitter

Wadanda aka shigar ƙara

Waɗanda aka shigar da ƙara sun haɗa da jam'iyyar ADC, David Mark, Patricia Akwashiki, Bolaji Abdullahi, Rauf Aregbesola, Oserheimen Osunbor (a madadin kwamitin riƙo na kasa), da kuma INEC.

Daga cikin buƙatun masu ƙarar akwai kalubalantar matakin shugabancin Sanata David Mark na kafa kwamitoci domin gudanar da zaben shugabannin jam'iyyar a matakin jihohi.

ADC ta bukaci a binciki Nafiu Bala

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC mai adawa ta bukaci hukumar zabe ta INEC da ta binciki Nafiu Bala.

Jam'iyyar ADC ta bukaci a binciki Nafi'u Bala bayan ya yi ikirarin yin amfani da takardun INEC na bogi wajen dora sunayen 'yan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng