Gowon Ya Ci Gyaran Wasu Yan Najeriya, Ya Fadi Yadda Buhari Ya Mulki Kasa

Gowon Ya Ci Gyaran Wasu Yan Najeriya, Ya Fadi Yadda Buhari Ya Mulki Kasa

  • Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya ce marigayi Muhammadu Buhari ya bayyana salon yadda marigayin ya yi mulki
  • Gowon ya ce Buhari ya sadaukar da mulkinsa wajen yi wa daukacin 'yan Najeriya hidima, ya ce ra'ayin cewa ya fifita Arewa ba gaskiya ba ne
  • Tsohon shugaban ƙasar ya kuma yabawa Goodluck Jonathan saboda amincewa da sakamakon zaɓen 2015 cikin lumana, yana cewa hakan ya taimaka wajen kauce wa rikici.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Janar Yakubu Gowon mai ritaya ya kare salon mulkin marigayi tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Tsohon shugaban kasar ya ce Buhari ya jagoranci Najeriya ba tare da nuna son kai ga wani yanki ba.

Gowon ya yabawa salon mulkin Buhari
Marigayi Muhammadu Buhari da Yakubu Gowon. Hoto: X/MBuhari, StanleyNkwocha.
Source: Twitter

Gowon ya bayyana hakan ne ranar Litinin a Abuja yayin bikin cika shekara ɗaya da rasuwar Buhari, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

'Buhari ya yi mulki irin wanda Musulunci ya nemi a yi': Alhassan Ado Doguwa

Gowon ya yaba salon mulkin marigayi Buhari

Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya ya ce marigayin ya kasance mai kishin hidimtawa dukkan 'yan Najeriya.

A cewarsa, salon mulkin Buhari ya ginu ne kan adalci da kuma ƙoƙarin inganta rayuwar al'umma ba tare da la'akari da yankin da mutum ya fito ba.

Ya ce Buhari ya kula da mutanen ƙasar baki ɗaya, ba wai mazauna Arewa kaɗai ba, ya ƙara da cewa manufarsa ita ce yi wa kowa aiki.

Gowon ya fadi kalar mulkin da Buhari ya yi
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari kafin rasuwarsa. Hoto: Malam Garba Shehu.
Source: Twitter

Gowon ya yi fatali da rahoton da ake yadawa

Gowon ya yi watsi da ra'ayin da wasu ke yaɗawa cewa Buhari shugaban Arewa kaɗai ne, ya ce ya tabbatar da cewa an yi wa dukkan jihohi da yankuna adalci.

Ya bayyana wannan a matsayin babban abin yabawa a tarihin Buhari. Ya kuma gode wa waɗanda suka halarci bikin tunawa da marigayin saboda girmama gudummawar da ya bayar.

Da yake tuna zaɓen shugaban ƙasa na 2015, Gowon ya ce yana taron Tarayyar Afirka a Addis Ababa lokacin da aka nuna fargabar barkewar rikici a Najeriya.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya nema a wurin Sheikh Karibullah a lokacin yana shugaban kasa

Ya ce tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya bayan ya amince da shan kaye tun kafin a bayyana sakamakon ƙarshe.

An haifi Muhammadu Buhari ranar 17 ga Disamba, 1942, a Daura da ke Katsina. Ya shiga aikin soja a 1961 kafin daga bisani ya shiga siyasar dimokuraɗiyya.

Buhari ya rasu ranar 13 ga Yulin 2025 yana da shekara 82 a wani asibiti da ke Landan bayan fama da doguwar rashin lafiya.

Al'ummar Najeriya da dama sun nuna alhini game da mutuwar marigayin wanda ya shafe shekaru takwas yana mulki, cewar Punch.

An yi taron tunawa da Buhari

An ji cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa tasirin marigayi Muhammadu Buhari na ci gaba da bayyana a Najeriya bayan shekara guda da rasuwarsa.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilci Tinubu a taron addu'ar tunawa da Buhari da aka yi Abuja ranar Litinin 13 ga watan Yulin shekarar 2026.

An sanar da kafa wata gidauniya don kiyaye tarihin tsohon shugaban kasar, yayin da Yakubu Gowon da sauran manyan mutane suka halarci taron.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.