"Shin Rasha ta Kashe Sanatan Amurka"; An Fara Nuna Yatsa kan Mutuwar Aminin Trump
- An fara kira da a gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar Sanata Lindsey Graham na jam'iyyar Republican a Amurka
- Masu wannan ra'ayi sun yi zargin ko an ba shi guba, amma ba su gabatar da wata hujja da ta tabbatar da hakan ba
- An ambaci barazanar da wasu jami'an Iran suka yi masa a baya da kuma matsayinsa kan yaƙin Rasha da Ukraine
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Washington, D.C., Amurka – An fara kira da a gudanar da cikakken bincike kan rasuwar Sanata Lindsey Graham bayan ya rasu sakamakon abin da ma'aikatansa suka bayyana a matsayin "gajeriyar rashin lafiya mai zuwa ba-zata."
An danganta mutuwarsa da barazanar kisa da wasu jami'an Iran suka yi masa a kwanakin baya, da kuma matsayinsa na goyon bayan ƙarin takunkumi kan Rasha da kuma goyon bayan Ukraine.

Source: Getty Images
Wata 'yar jarida a Amurka mai suna Laura Loomer ta yi wadannan zarge-zarge a shafinta na X a ranar Lahadi, 12 ga watan Yulin 2026.
Laura Loomer ta ambaci barazanar da wasu jami'an Iran suka yi masa a baya da kuma matsayinsa kan yaƙin Rasha da Ukraine
Sai dai har zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukumomi da ke nuna cewa an kashe Graham ko kuma an ba shi guba.
Me ya sa ake neman bincike?
Laura Loomer ta ce Rasha ta aika tawaga zuwa jana'izar tsohon jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, inda suka yi ikirarin cewa wasu daga cikin mahalarta jana'izar sun yi kira da a kashe Shugaba Donald Trump da Sanata Lindsey Graham.
Ta kuma ce Graham ya dawo daga Ukraine ne kwana ɗaya kacal kafin rasuwarsa, bayan ya yi kira da a ƙara kakaba wa Rasha takunkumi tare da ci gaba da bai wa Ukraine goyon baya.
A cewarta, mutuwarsa cikin gaggawa bayan ma'aikatansa sun ce ya kamu da "gajeriyar rashin lafiya ta ba-zata" ta sa ya dace hukumomi su gudanar da bincike domin tabbatar da abin da ya faru.
An nuna yatsa ga Rasha kan mutuwar Graham
"Shin Rasha ta sanya guba ga Lindsey Graham?"
"Ya kamata a gudanar da bincike. Rasha ta tura tawaga zuwa jana'izar Khamenei a Tehran inda IRGC da masu shirya janaizar suke kiran a kashe ni, Shugaba Trump da Sanata Graham."
"Lindsey Graham yana Ukraine kwana guda da ya wuce inda ya yi kira kan kudirin kakaba takunkumi ga Rasha wanda ya yi ikirarin White House na goyon baya."
"Yanzu kuma kwatsam ya mutu daga wata wuta a cewa ma'aikatansa. Shin Rasha ta kashe sanatan Amurka?"
An yi zargin ko an ba Graham guba
Laura Loomer ta tambayi abin da ake nufi da "gajeriyar rashin lafiya ta ba-zata", suna masu hasashen ko wata ƙasa ta ba Graham guba yayin tafiyarsa zuwa ƙasashen waje ko kuma bayan dawowarsa Amurka.

Source: Getty Images
Haka kuma, Laura Loomer ta ambaci cewa Alexander Dugin, wanda ake bayyana a matsayin ɗaya daga cikin masu ba Shugaban Rasha Vladimir Putin shawara, ya taɓa yin kalaman suka kan Lindsey Graham tare da cewa duniya za ta fi kyau idan babu shi.
Duk da haka, babu wata hujja da ta danganta rasuwarsa da Rasha, Iran ko wata ƙasa, kuma har yanzu hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da sakamakon wani bincike da ke tabbatar da waɗannan zarge-zarge ba.
Kwamandan IRGC ya sha alwashi kan Amurka, Israila
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran (IRGC), Birgediya Janar Ahmad Vahidi, ya sha alwashin daukar fansa kan Amurka da Isra'ila.
Birgediya Janar Ahmad Vahidi ya sha alwashin daukar fansar ne bayan kashe Jagoran addini a Iran, Ayatollah Ali Khamenei.
Asali: Legit.ng


