Duniya za Ta Huta: Trump Ya Ce Yaki da Iran Ya Zo Karshe, Babu Sauran kai Hari

Duniya za Ta Huta: Trump Ya Ce Yaki da Iran Ya Zo Karshe, Babu Sauran kai Hari

  • Shugaba Donald Trump ya yi ikirarin cewa Amurka ta kammala yaƙi da Iran, bayan ya sanar a ranar Alhamis cewa an cimma matsaya
  • Trump ya ce an yi wani babban sulhun da ya ce zai kawo ƙarshen rikicin da ake da kasar Iran tare da sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz
  • Ya kuma kara da cewa mataimakin shi, JD Vance, na iya halartar bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a Turai cikin kwanaki masu zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Iran ta amince da daina ƙera makaman nukiliya da daina sayen su a matsayin wani ɓangare na tattaunawar da ake ci gaba da yi.

Da yake magana ta wayar tarho da magoya bayansa, Trump ya ce fahimtar juna ta farko da suka yi da Iran ta shafi hana ƙera makaman nukiliya ne kawai.

Kara karanta wannan

'Maganar nukiliya ta kau': Trump ya sha alwashi kan ƙasar Musulunci ta Iran

Shugaban Amurka, Donald Trump
Donald Trump yana bankwana da Amurkawa a lokacin da zai yi tafiya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

“Yaki da Iran ya kare,”Trump

CNN ta wallafa cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yi ikirarin cewa Amurka ta gama yaƙi da Iran a jiya Alhamis, bayan ya bayyana tun da farko cewa ɓangarorin biyu sun amince da wata takardar fahimtar juna domin dakatar da faɗa.

“Ban sani ba ko kun ji, amma mun kawo ƙarshen yaƙi da Iran yau (Alhamis),”

In ji Trump yayin wani taron wayar tarho na goyon bamyan ataimakin gwamnan jihar Georgia, Burt Jones da ke neman kujerar gwamna.

“Sun amince ba za su taɓa mallakar makamin nukiliya ba, abin da muka dage a kai; wannan shi ne babban manufar. Kashi 95 cikin 100 na batun kenan.”

Iran ta yi wa Trump martani

A ranar Alhamis shugaba Donald Trump ya ce Washington da Tehran na iya sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tun a wannan ƙarshen mako, abin da zai iya sa a sake buɗe mashigar Hormuz.

Kara karanta wannan

Iran ta rufe Hormuz gaba daya, ta farmaki jiragen da suka yi taurin kai

Roya News ta wallafa cewa kasar Iran ta nuna cewa har yanzu ba a yanke hukunci na ƙarshe kan yarjejeniyar da aka gabatar ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce an riga an amince da yawancin abubuwan da ke cikin daftarin yarjejeniyar, amma ya jaddada cewa Tehran ba za ta yarda a danne ta ba.

“Har yanzu ba mu kai ga matsaya ta ƙarshe a wannan batu ba,”

In ji Baghaei, yana mai ƙarawa da cewa har yanzu hukumomin da suka dace a Iran na nazarin shirin.

Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei
Mojtaba Khamenei da wasu 'yan kasar Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Karin bayani daga Trump

Da yake magana a Fadar White House, Trump ya shaida wa manema labarai cewa yanzu haka sun cimma wani babban sulhu game da yaƙin Iran.

Lokacin da aka tambaye shi ko Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya amince da tsarin yarjejeniyar, Trump ya amsa da cewa:

“Abin da na fahimta shi ne eh.”

Trump ya soke kai hari Iran

A wani labarin, kun ji cewa a ranar Alhamis shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kai wa Iran wani mummunan hari.

Kara karanta wannan

"Za su dandana kudarsu"; Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran bayan musayar hare hare

Ya yi barazanar kai hare-hare da kuma yiwuwar karɓe iko da tsibirin Kharg, babban tashar fitar da mai da ke gabar tekun Iran.

Sai dai shugaban ya fito ya janye daga barazanar, inda ya ce kasashe da dama ciki har da Saudiyya, sun yi yarjejeniya da Iran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng