Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin fara anfani da fasahar makamashin nukiliya
Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bayyana cewa yanzu dai kama ta kammala shirye-shiryen duk da suka wajaba domin fara anfani da fasahar makamashin nukiliya wajen samar da wutar lantarki ga 'yan kasar.
Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da Mista Dmitry Shornikov da ke zaman babban masani kuma jami'an dake da kula da harkokin fasahar nukiya na kasar Rasha ya fitar ya turawa majiyar mu a ranar Talatar da ta gabata.
KU KARANTA: Labarin wata mata mai sana'ar tuka keke napep a Najeriya
Legit.ng ta samu cewa Mista Dmitry ya kara da cewa yanzu kasar saura kiris ta kammala cika duka sharuddan kaddamar da fasahar.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Aminu Tambuwal ya yi tsokaci tare da tambihi mai daukar hankali a game da kashe-kashen da ke aukuwa a kusan dukkan sassan kasar nan inda ya bayyana cewa ba abun da talakawan kasar suka zaba ba kenan a shekarar 2015.
Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake nuna alhinin sa akan mutane sama da 30 da wasu 'yan bindiga suka kashe a kauyen karamar hukumar Rabbah ta jihar Sokoto.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng