Sace Dalibai: Abu Ya Girma, Gwamna Ya Kai Korafi gaban Majalisar Dinkin Duniya
- Gwamna Seyi Makinde ya tura bukata ta musamman ga Majalisar Ɗinkin Duniya da hukumomin duniya kan sace ɗalibai
- Makinde ya ce binciken ba don raina hukumomin Najeriya ba ne, sai dai domin tabbatar da gaskiya da hukunta duk masu hannu
- Gwamnan ya ce 'yan Najeriya sun cancanci sanin abin da ya faru da kuma matakan hana sake afkuwar irin wannan hari kan makarantu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ibadan, Oyo - Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilin da ya sa ya bukaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta binciki sace dalibai.
Makinde ya bukaci majalisar da sauran hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa su binciki sace ɗalibai da malamai a ƙaramar hukumar Oriire.

Source: Twitter
Makinde ya yi wannan bayani ne a jawabin da ya yi wa al'ummar jihar bayan an ceto ɗaliban da malamansu cikin nasara, cewar Tribune.
Bukatar Gwamna Makinde ga Majalisar Dinkin Duniya
Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan lamari ya cancanci bincike mai zaman kansa daga hukumomin duniya domin gano cikakken gaskiyar abin da ya faru da yadda aka warware matsalar.
A cewarsa, shigar da hukumomin kare haƙƙin ɗan Adam na duniya, ciki har da na Majalisar Ɗinkin Duniya, zai ƙara tabbatar da gaskiya tare da ƙarfafa amincewar jama'a da sakamakon binciken.
Gwamnan ya ce wannan mataki ba don raunana hukumomin Najeriya ba ne. Ya ce manufarsa ita ce tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi, ko wanene, za a hukunta shi.
Lamarin sace dalibai da kuma hare-haren yan bindiga ya jawo rarrabuwar kai a Oyo yayin da ake zargin gwamnati kafin sakin daliban.

Source: Original
Gwamna ya bukaci bincike kan sace dalibai
Makinde ya tuna cewa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya ɗora alhakin tsaron ƙasa a kan gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da ke ƙarƙashinta.
Ya ce 'yan Najeriya sun cancanci cikakken bayani kan abin da ya faru, ko akwai gazawa, sakaci ko haɗin baki daga wata hukuma, da kuma matakan hana sake aukuwar irin wannan hari, cewar Punch.
Gwamnan ya ƙara da cewa babban burinsa shi ne a samu adalci ga waɗanda abin ya shafa, a kwantar wa al'umma hankali, tare da dawo da amincewar cewa kowane yaro a Najeriya zai iya zuwa makaranta ba tare da tsoro ba.
Rahotanni sun nuna cewa an sace ɗaliban da malamansu ne a ranar 15 ga Mayu bayan 'yan bindiga sun kai hari makarantu uku da ke ƙaramar hukumar Oriire, lamarin da ya jawo fargaba a tsakanin al'ummar jihar Oyo.
Oyo: Yan bindiga sun sace shugaban makaranta
A wani labarin, an ji cewa rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga sun sace shugaban wata makarantar firamare a ƙaramar hukumar Itesiwaju da ke jihar Oyo.
An ce masu garkuwa da mutanen sun nemi Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansar shugaban makarantar bayan sun tuntuɓi iyalansa.
Yayin da aka samu bayanai kan sace shi, 'yan sandan Oyo sun tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ana kan kokarin ceto shi.
Asali: Legit.ng

