Bayan Tinubu Ya Aika Sako, Majalisa Ta Janye Kudirinta kan Kafa Yan Sandan Jihohi a Najeriya
- Majalisar Wakilai ta tarayya ta janye kudirinta da ta fara karatu a kansa kan batun kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeirya
- Ta dauki wannan mataki ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya tura nasa kudirin kan wannan batu a zaman yau Talata
- ‘Yan majalisar dokokin na kasa sun amince da karatu na farko da na biyu ga kudirin da Tinubu ya gabatar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Majalisar Wakilai ta janye kudirinta gyaran kundin tsarin mulki da ta gabatar domin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya.
Majalisar ta kuma yanke shawarar ba da fifiko da rungumar irin wannan kudiri da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aikewa majalisar yau Talata.

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an cimma wannan matsaya ne bayan tattaunawa a zaman majalisar na ranar Talata, 14 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan
'Yan sandan jihohi: Tinubu ya aika da bukatar gyara kundin tsarin mulki ga majalisa
Tun farko dai Shugaba Tinubu ya mika wa Majalisar kudirin neman gyara kundin tsarin mulki, wanda zai ba da damar kafa runfunar yan sandan jihohi a Najeriya.
Majalisar wakilai ta janye nata kudirin
Shugavan Majalisar wakilan tarayya, Rt. Hon Tajudeen Abbas ne ya karanta sakon Tinubu, wanda hakan ya sa Majalisar ta janye nata kudirin tare da rungumar na shugaban kasa
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa bayan Tinubu ya gabatar da kudirin, ‘yan majalisar sun yi wa kudirin ma bangaren zartarwa karatu na farko da na biyu.
Bayan kammala karatun, an mika kudirin ga Kwamitin Majalisar kan Gyaran Kundin Tsarin Mulki domin yin cikakken nazari a kansa.
Majalisa ta dauki kudirin Shugaba Tinubu
Wannan mataki na nuni da sauyin akalar da Majalisar Wakilai ta dauka kan batun kafa ‘yan sanda na jihohi, bayan ta dakatar da aiki kan nata kudirin tare da ba wa na Shugaba Tinubu fifiko.
Da wannan matsaya, majalisar ta dakatar da ci gaba da duba kudirinta na baya, tare da bai wa kudirin shugaban kasa damar ci gaba da tafiya cikin tsarin majalisa.
Kwamitin Majalisa zai yi cikakken nazari
Ana sa ran Kwamitin Gyaran Kundin Tsarin Mulki zai yi cikakken nazari kan muhimman tanade-tanaden kudirin da tasirinsa ga kundin tsarin mulki.
Bayan kammala bincike da nazarin, kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga Majalisar Wakilai domin ci gaba da muhawara da kuma yanke hukunci kan yiwuwar amincewa da kudirin.

Source: Facebook
Matakin na daga cikin ci gaba da kokarin gyara Kundin Tsarin Mulkin 1999 domin samar da cikakkiyar doka da za ta ba da damar kafa rundunar ‘yan sanda ta jihohi.
Bukatar kafa ‘yan sanda na jihohi ta kara samun karbuwa a Najeriya sakamakon karuwar matsalar tsaro da kuma kiraye-kirayen da ake yi na bai wa jihohi karin iko wajen kula da harkokin tsaro a yankunansu.
Majalisar dattawa ta amince da kudirin Tinubu
Kun ji cewa Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudirin kafa ‘yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.
Matakin ya kasance daya daga cikin manyan sauye-sauyen da ake jira na tsarin tsaro, musamman a daidai lokacin da ake fama da kalubale iri daban-daban.
Amincewar majalisar na zuwa ne bayan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya mika mata bukatar kafa rundunar yan sandan jihohi a Najeriya.
Asali: Legit.ng
