Kasar Rasha Ta Kawo Mafita ga Shirin Nukiyar Iran, Abin bai Yi Wa Amurka Dadi ba

Kasar Rasha Ta Kawo Mafita ga Shirin Nukiyar Iran, Abin bai Yi Wa Amurka Dadi ba

  • Rasha ta bayyana cewa ta gabatar da tayin kwashe duka sindarin Uranium na Iran domin samar da mafita a tattaunawar sulhu da Amurka
  • Sai dai fadar Kremlin ta ce gwamnatin Amurka ba ta ji dadin wannan shawara ba kuma ta yi fatali da ita nan take
  • Bayanai sun nuna cewa Shugaba Vladimir Putin na Rasha na duba yiwuwar sake gabatar da wannan tayi idan bukatar hakan ta taso

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Russia - Kasar Rasha ta yi yunkurin kawo mafita kan shirin nukiliyar Iran, wanda ke ci gaba da zama kalubale a zaman tattaunawar sulhun da aka fara tsakanin Amurka da Iran.

Rasha ta gabatar da tayin dauke duka sindarin Uranium da Iran ta mallaka domin kawo karshen takaddamar kasar da Amurka, wanda shi ne babban abin da ya dakile shirin sulhu.

Kara karanta wannan

Trump: A karo na 4, majalisar Amurka ta sake kuri'a kan yaƙi da Iran

Shugaban Rasha, Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a fadar gwamnatinsa Hoto: Alexander Kazakov
Source: Getty Images

Amurka ta yi fatali da shawarar Rasha

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa Amurka ba ta yarda da wannan shawara ta Rasha ba, amma duk da haka alamu sun nuna Shugaba Vladimir Putin zai sake mika wannan bukata.

Mai magana da yawun fadar Kremlin, Dmitry Peskov, ne ya bayyana hakan, inda ya ce Amurka ta ƙi amincewa da shawarar da Rasha ta gabatar na ɗaukar dukkan uranium da Iran ta tace daga ƙasar.

Shawarar Rasha da aka yi watsi da ita

Peskov ya ce Rasha ta nuna shirin karɓar Uranium ɗin Iran a cikin ƙasarta, domin rage fargaba, ta kuma taimaka wajen warware rikicin da ke faruwa a yankin.

A cewarsa, wannan shawara za ta iya zama hanya mai kyau ta samar da mafita, amma Amurka ta yi watsi da ita.

“Rasha a shirye take ta karɓi Uranium da Iran ta tace a cikin ƙasarta. Wannan zai kasance kyakkyawar mafita. Amma abin takaici, ɓangaren Amurka ya ƙi aminfa da wannan shawara,” in ji Peskov.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jirgin Iran ya kutsa wajen da Trump ya jibge sojoji a Hormuz

Shugaba Putin zai sake gabatar da tayin

Ya ƙara da cewa Shugaban Rasha, Vladimir Putin, har yanzu a shirye yake ya dawo da wannan shiri idan ƙasashen da abin ya shafa suka ga ya dace.

Peskov ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi, inda ya ce akwai muhimmancin komawa ga asalin matsalar da ta faro a yankin Tekun Fasha domin nemo mafita mai ɗorewa.

Shugaban Rasha.
Shugaban Rasha, Vladimir Putin lokacin da ya karbi bakuncin takwaransa na Amurka, Donald Trump Hoto: Andrew Harnik
Source: Getty Images

Rikicin nukiliyar kasar Iran

Batun shirin nukiliyar Iran na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa takaddama tsakanin ƙasar da Amurka da kawayenta, inda Amurka ke son hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Sai dai Iran ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na zaman lafiya ne kawai, ba na kera makamai ba, kamar yadda Reuters ta kawo a rahotonta.

Rasha ta amfana da yakin Iran da Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa wani rahoto ya gano cewa Shugaban Rasha, Vladimir Putin, na samun kudin shiga mai yawa sakamakon rikicin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

JD Vance ya fito da gaskiya, an ji matakin Iran da ya fi cutar da Amurka a lokacin yaki

Wannan karin kudi ya samu ne daga sayar da mai yayin da rikicin Iran ke ƙara jawo cikas ga safarar makamashi a fadin duniya.

A wani taro da aka gudanar a Kremlin, Putin ya bukaci kamfanonin mai da gas na Rasha su yi amfani da karin kudin da suka samu wajen rage basussukansu a cikin gida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262