Dalibai Sun Tsere, Iyaye Sun Kidime bayan Rahoton Yan Bindiga Sun Kutsa Makarantu a Neja

Dalibai Sun Tsere, Iyaye Sun Kidime bayan Rahoton Yan Bindiga Sun Kutsa Makarantu a Neja

  • Iyaye da wasu daga cikin makarantu a jihar Neja sun shiga damuwa bayan an samu bullar labarin ƴan bindiga sun shiga gari
  • Dalibai da dama sun bar makarantu kafin lokacin tashi saboda tsoron ƴan bindiga za su iya zuwa su yi garkuwa da su
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta kwantar da hankalin jama'a, inda ta bayyana cewa tana ci gaba da aikin kare rayukansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Jama'a sun shiga cikin yanayin firgici a birnin Minna na jihar Neja bayan wata jita-jita ta bazu cewa ‘yan bindiga sun kutsa cikin birnin tare da kai hari kan wasu makarantu.

Lamarin ya sa ɗalibai da almajirai da dama suka bar azuzuwansu cikin gaggawa a ranar Laraba, 10 ga watan Yuni, 2026 ba tare da jiran lokacin tashi daga makaranta ba.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna ya umarci rufe makarantu bayan samun rahoton DSS

Iyaye sun rude bayan zargin yan bindiga sun shiga makarantu a jihar Neja
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago Hoto: Umaru Mohammed Bago
Source: Twitter

Rahotannin da jaridar Punch ta samu sun nuna cewaa lokacin da labarin ya bazu, iyaye sun fara kira zuwa makarantu domin tabbatar da halin da ‘ya’yansu ke ciki da kuma ko an rufe makarantu saboda barazanar tsaro.

Iyaye sun rude a jihar Neja

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa wasu iyaye sun garzaya makarantu domin ɗaukar ‘ya’yansu zuwa gida saboda tsoron kada wani abu ya faru daga baya.

Haka kuma wasu shugabannin makarantu sun ce sun samu kira da dama daga iyaye masu neman karin bayani kan halin da ake ciki.

Wata shugabar makaranta a yankin ta bayyana cewa ta ji jita-jitar kamar kowa, amma ba ta ga wata alamar harin ‘yan bindiga ba.

Ta ce har ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar domin samun tabbaci, inda aka gaya mata cewa babu irin wannan hari.

‘Yan sanda sun musanta rahoton hari a Neja

A martaninta, rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta bayyana cewa rahotannin da ke yawo na cewa an kai hari kan makarantu a yankunan Bosso, Kpakungu, Sabon-Wuse da Lambata ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Takardun kotu sun nuna yadda tsohon Akanta Janar a Bauchi ya 'wawur' N40bn

Mai magana da yawun rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya ce jami’an tsaro sun ziyarci makarantun da aka ambata kuma sun tabbatar da cewa babu wata makaranta da aka kai wa hari.

Ya ce rundunar na kira ga jama’a da su yi watsi da rahotannin karya da ake yadawa domin haddasa tsoro da firgici a tsakanin mazauna jihar da kuma al’ummar makarantu.

Abiodun ya kuma bayyana cewa an fara bincike domin gano tushen jita-jitar da kuma kamo mutanen da ke da hannu wajen yada bayanan karya.

Ya kara da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar Neja, Adamu Elleman, ya umarci jami’an ‘yan sanda da su ci gaba da hada kai da shugabannin makarantu domin tabbatar da tsaron ɗalibai, malamai da sauran al’umma.

Rundunar ƴan sanda ta ƙaryata labarin hari a Neja
Sufeton ƴan sandan Najeriya, Tunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Duk da bayanin da ‘yan sanda suka bayar, wasu iyaye sun ce har yanzu suna cikin fargaba sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da sace ɗalibai a wasu sassan ƙasar nan.

Sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro su kara daukar matakan kare makarantu da rayukan yara da ke neman ilimi.

An cafke masu hannu a sace daliban Neja

A baya, mun wallafa cewa hukumar DSS ta cafke wasu mutane da ake zargi da safarar makamai ga ‘yan bindigar da suka sace ɗaliban makarantar Katolika ta Papiri a jihar Neja.

Kara karanta wannan

Asirin matar aure ya tonu, an gano tana sheke aya a otal bayan an tara N20m kudin fansa

Hukumar tsaron fararen kayan ta gano cewa daga cikin mutanen da ta kama akwai 'yan kasar waje guda biyu da kuma wasu masu alaka da kungiyar ta'addan Boko Haram.

Jami'an sun yi nasarar kwato miyagun makamai da suka hada da bindigu ƙirar AK-103 guda 15, mujallu 15 da harsasai da suka haura 1000 yayin da ake farautar sauran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng