Kisan Khamenei: Iran Ta Fitar da Sunan Trump da Shugabanni 13 da Za Ta Dauki Fansa

Kisan Khamenei: Iran Ta Fitar da Sunan Trump da Shugabanni 13 da Za Ta Dauki Fansa

  • Wasu majiyoyi a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta wallafa wasu shugabannin duniya da za ta dauki fansa kansu
  • An wallafa jerin shugabannin kasashen waje 13 da ta ce za a dauki fansa a kansu bayan kashe marigayi Jagoran Koli Ayatollah Ali Khamenei
  • Sabon Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei ya ce daukar fansa shi ne muradin al'ummar kasar baki daya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Ana ci gaba da fito da bayanai game da daukar fansar jinin tsohon jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an wallafa sunayen shugabannin kasashen waje da ake zargin suna da hannu.

Shugabannin kasashen da Iran ya jero domin daukar fansa
Shugaba Donald Trump na kasar Amurka. Hoto: @RealDonaldTrump.
Source: Twitter

Rahoton Hisdustan Times ta bayyana cewa mutanen da ke cikin jerin su ne ake son daukar fansa a kansu bayan kashe marigayi Jagoran Koli na Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Kara karanta wannan

Ana zargin yaran Dogo Gide sun rage mugun iri, an hallaka hatsabibin dan bindiga

Alwashin da Mojtaba Khamenei ya sha

An ce hare-haren hadin gwiwar Amurka da Isra'ila ne suka kashe Ayatollah Ali Khamenei ranar 28 ga Fabrairu, ranar farko ta yakin Gabas ta Tsakiya.

Bayan rasuwar mahaifinsa, sabon Jagoran Koli Mojtaba Khamenei ya yi alkawarin daukar fansa, inda ya fitar da sakonsa na farko tun bayan jana'izar da aka yi.

Ya ce daukar fansa shi ne muradin al'ummar Iran, yana mai cewa dole ne a aiwatar da hakan, kuma wadanda ke cikin jerin ba za su mutu cikin kwanciyar hankali ba.

Jaridar Hamshahri, wacce hukumomin birnin Tehran ke bugawa, ta wallafa hotunan shugabannin kasashen waje 13 tare da kalaman Mojtaba Khamenei a wani hoto mai bayanai.

Sai dai Mojtaba bai ambaci sunayen mutanen da ake nufi ba, kuma babu wata alama da ke nuna gwamnatin Iran ta amince da jerin sunayen jaridar.

Jerin wadanda Iran take fako kan kisan Ali Khamenei
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei, Shugaba Donald Trump na Amurka da Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump, Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Jinin Khamenei: Jerin wadanda Iran ke fako

Jerin ya hada da Shugaban Amurka Donald Trump, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, Firaministan Birtaniya Keir Starmer da wasu shugabannin Turai.

Kara karanta wannan

Alaka ta munana: An hada baki da sojoji aka tsare dan majalisar Amurka a Isra'ila

Sauran sun hada da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio, Ministan Tsaron Amurka Pete Hegseth, Shugaban Faransa Emmanuel Macron.

Haka kuma akwai Firaministar Italiya Giorgia Meloni da Kansilan Jamus Friedrich Merz cikin jerin shugabannin da jaridar ta wallafa wanda Punch ta gano.

A lokacin yakin, Iran ta zargi wasu kasashen Turai da kin yin Allah wadai da hare-haren da aka kai mata da kuma bai wa jiragen yakin Amurka damar amfani da sararinsu.

Rahotanni sun kuma ce ba a ga Mojtaba Khamenei a bainar jama'a ba tun kafin barkewar yakin, kuma an ce ya samu raunuka a harin da ya kashe mahaifinsa.

Iran ta kai hari kan sansanonin Amurka

An ji cewa Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan hare-haren da sojojin Amurka suka kai a wasu sassan yankinsu ranar Laraba 8 ga watan Yulin 2026.

Sojojin Amurka sun bayyana cewa harin martani ne bayan Iran ta kai hari kan jiragen kasuwanci uku da ke bi ta mashigar Hormuz ranar Talata 7 ga watan Yulin 2026.

Wannan musayar wuta ta sake kamari yayin da Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Kuwait bayan farmakin Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.