Abba Ya Aika Tawaga zuwa Jihar Sakkwato bayan Rasuwar Sardauna

Abba Ya Aika Tawaga zuwa Jihar Sakkwato bayan Rasuwar Sardauna

  • Gwamnatin Kano tkarkashin Abba Kabir Yusuf, a kai ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Musulmi da gwamnatin Sakkwato kan rasuwar Sardauna
  • Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, ya jagoranci tawagar da ta isar da saƙon ta'aziyyar Gwamna Abba Kabir Yusuf
  • Sarkin Musulmi ya yaba da wannan ziyara, yana mai cewa ta nuna haɗin kai da ƴan'uwantaka tsakanin al'ummar Arewacin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uk u. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta kai ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, da gwamnatin da al'ummar Jihar Sakkwato bisa rasuwar Sardauna, Alhaji Abubakar Alhaji.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sunusi Bature Tofa, ya fitar a ranar Talata, inda ya bayyana cewa an gudanar da ziyarar ne a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Yusuf ya gwangwaje hadimansa, ya raba masu manyan filaye a Kano

Gwamnatin Kano ta tura tawaga Sakkwato
Murtala Sule Garo da tawagar da ta kai ziyara Sakkwato Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Sanarwar da Sanusi Bature Dawakin Tofa, hadimin gwamnan ya wallafa a Facebook ta ce tawagar ta samu jagorancin Mataimakin Gwamnan Kano, Murtala Sule Garo, tare da Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Ibrahim.

Tawagar gwamnatin Kano ta je Sakkwato

Sauran wadanda suka kai ziyarar sun hada da, Sarkin Rano, Muhammad Umar, Shugaban APC na Kano, Umar Haruna Doguwa, Kwamishiniyar Al'adu da Yawon Buɗe Ido, Aisha Saji, da wasu manyan jami'an gwamnati.

Tawagar gwamnatin Kano ta ziyarci Sarkin Musulmi
Tawagar gwamati lokacin da ta mika ta'aziyya a madadin gwamantin Kano Hoto: Sunusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Da farko tawagar ta kai ziyara gidan marigayi Sardaunan Sakkwato, inda ta miƙa saƙon ta'aziyyar Gwamna Abba Kabir Yusuf ga iyalan mamacin.

A madadin iyalan marigayin, babban ɗansa Aminu Abubakar ya gode wa gwamnan Kano bisa nuna alhini da jajantawa da ya yi musu a wannan lokaci na jimami.

Sakkwato: Tawagar Kano ta ziyarci Sarkin Musulmi

Daga nan tawagar ta zarce zuwa fadar Sarkin Musulmi, inda ta isar da saƙon ta'aziyyar gwamnan ga mai martaba Sarkin Musulmi.

Kara karanta wannan

Kosan Waka: An fitar da lokacin jana'izar fitaccen mawakin Gwamnan Kano

Sarkin Musulmin ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan karamci, yana mai cewa ziyarar ta nuna ƙarfi da ɗorewar haɗin kai da zumunci tsakanin al'ummar Arewacin Najeriya.

Ya ce:

"Muna godiya ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa wannan kyakkyawan mataki. Wannan ya nuna haɗin kai da ɗorewar ƴan'uwantaka da ke haɗa al'ummar Arewacin Najeriya."

Bayan haka tawagar ta kai ziyara gidan gwamnatin Jihar Sokoto, inda Mataimakin Gwamnan jihar da Sakataren Gwamnatin Jihar suka tarbe su.

A nan ma tawagar ta isar da saƙon ta'aziyyar Gwamna Abba Kabir Yusuf ga gwamnatin da al'ummar Sokoto bisa rasuwar fitaccen mai riƙe da sarautar gargajiya.

An kai hari Sakkwato

A baya, mun kawo labarin cewa ’yan kungiyar Lakurawa sun kai hari garin Girkau da ke karamar hukumar Kebbe a jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeriya, inda dama ake fama da yan bindiga.

Harin ya yi sanadin mutuwar jami’in dan sanda da fararen hula biyu, yayin da wasu suka samu raunuka, tare da barin sauran mazauna garin a cikin tashin hankali da neman tsira da rayukansu.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kuma kona motocin jami’an tsaro biyu mallakar rundunar ’yan sandan Najeriya da hukumar Sakkwato State Community Guard Corps.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng