Yadda Aka Tatsi Bayanai daga Wadanda Ake Zargi da Shirya Juyin Mulkin Tinubu

Yadda Aka Tatsi Bayanai daga Wadanda Ake Zargi da Shirya Juyin Mulkin Tinubu

  • Ana ci gaba da shari'ar game da zargin hannun wasu a yunkurin yi wa gwamnatin Bola Tinubu juyin mulki kwanakin baya
  • Wani shaidan gwamnati ya fada wa kotun tarayya da ke Abuja cewa wadanda ake zargi sun bayar da bayanansu bisa ka'ida
  • Lauyoyin wadanda ake kara sun dage cewa an karbi bayanan ne cikin matsin lamba, yayin da kotu ta ci gaba da sauraron karar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani shaidan gwamnati ya bayyana wa Babbar Kotun Tarayya yadda ake tatsar bayanai game da zargin wasu da hannu a yunkurin juyin mulki.

Shaidan ya bayyana cewa mutane shida da ake zargi da yunkurin juyin mulki sun bayar da bayanansu cikin son rai ba tare da wani matsin lamba ba.

Ana ci gaba da tatsar bayanai game da zargin juyin mulki
Shugaba Bola Tinubu yayin taro a birnin Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Shari’ar ta shafi zargin shirya hambarar da gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bayan bayanan sirri sun isa hannun hukumomi a watan Satumban bara, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Zamfara ta magantu da ake zargin harin jirgi ya kashe yan kasuwa 100

Ana zargin ana tatsar bayanan juyin mulki bisa tilas

Mai shari’a, Joyce Abdulmalik, ta dakatar da sauraron karar domin gudanar da shari’a cikin shari’a kan sahihancin bayanan da aka karba daga wadanda ake tuhuma.

Lauyoyin wadanda ake kara sun yi zargin cewa an karbi bayanan ne ta hanyar matsin lamba da tilastawa yayin binciken da jami’an tsaro suka gudanar.

Sai dai lauyan gwamnatin tarayya, Rotimi Oyedepo, ya ce gwamnati na da shaidu uku da za su tabbatar da cewa an bi ka’idojin doka wajen binciken.

Shaidan farko mai lakabin AAA saboda dalilan tsaro ya bayyana cewa an dauki bidiyon dukkan zaman tambayoyin da aka yi wa wadanda ake zargi.

Shaidan ya ce wadanda ake tuhuma sun kasance cikin natsuwa kuma sun san hakkokinsu na kundin tsarin mulki kafin bayar da bayanansu ga jami’an bincike.

Daya daga cikin malamai da ake zargi da hannu a juyin mulki
Shehin malami da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulki. Hoto: Sheikh Abdulkadir Sani Khalifa.
Source: Facebook

Wadanda ake tuhuma da zargin juyin mulki

Daga cikin wadanda ake kara akwai tsohon janar, Mohammed Ibrahim Gana, tsohon jami’in ruwa, Erasmus Ochegobia Victor, da sufeton ’yan sanda, Ahmed Ibrahim.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta faɗi tarkon da ta ke yi wa tubabbun Boko Haram da Kur'ani

Sauran sun hada da Zekeri Umoru, Bukar Kashim Goni da malamin addini, Abdulkadir Sani Khalifa da ke zaune a Zariya.

An tuhume su da laifuffuka 13 da suka hada da cin amanar kasa, ta’addanci, boye bayanai da kuma wanke kudade kan yunkurin juyin mulkin da ake zargi.

Shaidan ya ce babu wani daga cikin wadanda ake zargi da aka hana damar samun lauya, duk da cewa babu lauyoyi a lokacin daukar bayanansu.

Ya kuma bayyana cewa an samar da mai fassara daga Hausa zuwa Turanci ga daya daga cikin wadanda ake tuhuma saboda rashin iya Turanci sosai, cewar Punch.

Kotun ta dage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 13 ga watan Mayu domin ci gaba da tantance ko an bayar da bayanan cikin son rai ko akasin haka.

Juyin mulki: Sheikh Khalifa ya magantu a kotu

Mun ba ku labarin cewa babban malamin Musulunci a Zaria, Sheikh Sani Khalifa ya gabatar da bayani kan zargin da ake yi masa na hannu a shirin juyin mulki.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci, ta ci tarar wanda ya nemi a rushe babban taron APC na kasa

Bayanin shehin na darikar Tijjaniya na cikin wani faifan bidiyo da bangaren gwamnatin tarayya ya gabatar a zaman babbar kotun tarayya.

Malamin ya tabbatar da cewa an tuntube shi domin ya yi addu'a ga masu shirin juyin mulki, amma ya gargade su da cewa ba za su yi nasara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.