Jirgin Kasar Amurka Ya Ruguzo daga Sama Ya Kama da Wuta

Jirgin Kasar Amurka Ya Ruguzo daga Sama Ya Kama da Wuta

  • Matukin jirgin yaƙin F-35B na rundunar sojojin ruwan Amurka ya tsallake rijiya da baya bayan ya yi amfani da na'urar ceto kafin jirgin ya faɗi a California
  • Jirgin yaƙin na zamani mai darajar kusan dala miliyan 109 ya yi hatsari ne kusa da sansanin sojin Amurka da ke Miramar a San Diego
  • Rundunar sojojin ruwan Amurka ta tabbatar da cewa matukin jirgin na samun kulawa a asibiti bayan ya samu raunuka marasa haɗarin gaske

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America – Wani jirgin yaƙin F-35B na rundunar sojojin ruwan Amurka ya yi hatsari kusa da sansaninsu da ke San Diego a jihar California.

Hakan na zuwa ne yayin da Amurka ke cigaba da takun saka da Iran a Gabas ta Tsakiya tun watan Fabrairun 2026 har zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Netanyahu ya fadi matakin da sojojin Isra'ila za su dauka idan aka cafke shi

Jirgin Amurka na F-35B
Lokacin da jirgin Amurka ya kama da wuta bayan ya fado. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matukin jirgin ya samu damar amfani da na'urar ceto kafin jirgin ya faɗi, kuma an garzaya da shi asibiti domin duba lafiyarsa da kuma yi masa magani, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Yadda jirgin Amurka ya yi hatsari

Rundunar Amurka ta bayyana cewa an ayyana lamarin a matsayin ɗaya daga cikin manyan hatsurran jiragen sama na soji.

A cikin sanarwar da ta fitar, rundunar ta ce:

"Matukin jirgin ya yi amfani da na'urar ceto, sannan aka kai shi wani asibitin yankin inda ake kula da shi. Raunukan da ya samu ba su da haɗarin rasa rai."

Bidiyon da jirgin ɗaukar labarai ya ɗauka daga sama ya nuna hayaƙi baƙi yana tashi daga wurin da jirgin ya faɗi, yayin da motocin soji da na kashe gobara suka mamaye wajen.

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump na shirin shiga jirgi a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Bayanin shaidun gani da ido

Wani shaidar gani da ido ya ce ya ga jirgin yana shawagi sama da titin Interstate 15 kafin ya faɗi ya kama da wuta mai ƙarfi.

Kara karanta wannan

Iran ta kai kazamin hari, ta latata jiragen yaki da kashe sojojin Amurka

Independent ta rahoto cewa shaidar ta ce ya kuma ga laima tana sauka daga sama, wanda ake kyautata zaton ita ce ta matukin jirgin da ya yi amfani da ita.

Jirgin F-35B wani nau'i ne na jiragen yaƙin F-35 da rundunar Amurka ke amfani da shi, wanda aka ƙera domin iya tashi daga gajeren fili tare da sauka a tsaye, abin da ya sa yake da sauƙin gudanar da ayyukan soja a wurare daban-daban.

Yarjejeniyar Hamas da Trump

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da cewa kwamitinsa ya cimma yarjejeniya da ƙungiyar Hamas kan ajiye makamai da kuma mika ikon tafiyar da Gaza ga sabuwar gwamnatin farar hula ta Falasɗinu.

An bayyana cewa idan aka aiwatar da yarjejeniyar, za ta zama wani babban ci gaba a cikin shirin zaman lafiya na Trump mai matakai 20 domin kawo ƙarshen rikicin Gaza da kuma fara aikin sake gina yankin.

Sai dai jami'an Isra'ila na ci gaba da nuna gardama kan lamarin, yayin da ake sa ran aiwatar da yarjejeniyar cikin watanni bakwai zuwa takwas masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng