Bayan Shekara 3, an Samu Gawar Faladinawa 112 da Isra'ila Ta Kashe, an Masu Sallah
- An yi jana'izar Falasɗinawa 112 da aka gano gawarwakinsu bayan sun kwashe kusan shekaru uku a ƙarƙashin gine-gine a unguwar Sabra da ke birnin Gaza
- Jami'an Falasɗinu sun ce harin Isra'ila na Nuwamban 2023 ya kashe mutum 308 daga iyalan Abu Sharia da al-Hasayna, ciki har da yara 40 da mata 30
- Duk da birne gawarwakin, hukumomi sun ce har yanzu mutum kusan 157 na ci gaba da ɓacewa, yayin da ake zargin suna ƙarƙashin gine-gine da suka rushe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gaza – Dubban Falasɗinawa sun hallara domin gudanar da jana'izar mutum 112 da aka gano gawarwakinsu a zirin Gaza.
An gano su ne bayan sun shafe kusan shekaru uku a ƙarƙashin gine-gine sakamakon wani hari da Isra'ila ta kai a birnin Gaza.

Source: Getty Images
Al Jazeera ta rahoto cewa an gudanar da jana'izar ne bayan ƙungiyoyin ceto sun samu nasarar tono gawarwakin daga wurin da aka kai hari a unguwar Sabra tun ranar 22 ga Nuwamba, 2023.
Harin ya hallaka ɗaruruwan mutane
A cewar jami'an Falasɗinu, harin ya kashe mutum 308 daga iyalan Abu Sharia da al-Hasayna, ciki har da yara 40, mata 30 da kuma mutane bakwai masu nakasa.
Bayan shekaru ana ci gaba da aikin ceto, jami'an sun samu gawarwaki sama da 100, lamarin da ya bai wa iyalan mamatan damar gudanar da sallar jana'iza da birne su cikin mutunci.
Sai dai hukumomi sun bayyana cewa har yanzu mutum kusan 157 na ci gaba da ɓacewa, inda ake zargin wasu daga cikinsu na ƙarƙashin baraguzan gine-gine.
jana'izar ce mafi girma a Gaza
An ɗaura akwatunan gawarwakin da tutocin Falasɗinu yayin da dubban mutane suka raka su zuwa makabarta, tare da ɗauke da hotunan mamatan da kuma kira da a kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza.
Mai magana da yawun Hukumar Kare Fararen Hula ta Gaza, Mahmoud Basal, ya bayyana jana'izar a matsayin ɗaya daga cikin mafi girma da aka taɓa yi tun bayan fara yaƙin.

Source: Getty Images
Sakataren Janar na Palestinian National Initiative, Mustafa Barghouti, ya ce akwai yiwuwar wannan ta kasance mafi girman jana'iza a tarihin Falasɗinawa.
Har yanzu ana neman gawarwaki
Masu bincike da masu fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam sun bayyana cewa jana'izar ta sake nuna irin bala'in da iyalai da dama ke ciki, yayin da ake ci gaba da neman gawarwakin dubban mutanen da suka ɓace.
Shugaban Euro-Med Human Rights Monitor, Ramy Abdu, ya ce har yanzu ana kyautata zaton kusan mutum 200 daga iyalan Abu Sharia na ƙarƙashin gine-gine.
Hukumomin Falasɗinu sun ce tun bayan fara yaƙin a watan Oktoban 2023, an kashe aƙalla Falasɗinawa 73,375 tare da jikkata sama da 174,220, yawancinsu mata da yara.
Sun kuma ce kusan kashi 90 na abubuwan more rayuwa a Gaza sun lalace ko kuma an rushe su sakamakon yaƙin.
Ga bidiyon jana'izar da Ramu Abdul ya wallafa a X:
'Yar Falasdinu ta ci zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yar majalisar wakilan Amurka daga jihar Michigan, Rashida Tlaib, ta samu nasara a zaɓen fidda gwani na jam'iyyar Democrat domin sake neman kujerarta ta wakiltar mazabar 12 ta jihar.
Tlaib ta doke Shanelle Jackson da Byron Nolen, inda ta tabbatar da kasancewarta 'yar takarar jam'iyyar a babban zaɓen da za a gudanar ranar 3 ga watan Nuwamba.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa Tlaib ta samu nasarar ne bayan ta yi wa abokan hamayyarta fintinkau a jam'iyyar Democract.
Asali: Legit.ng


