Tinubu na Tsaka Mai Wuya, Babban Jigo Ya Tayar da Rigima a APC kan Takarar Shugaban Kasa a 2027
- Wani babban jigon APC, Alhaji Bayero Lawal, ya tayar da rigima ta hanyar maka jam’iyyarsa kotu kan batun takarar shugaban kasa a 2027
- Ya zargi jam'iyyar APC da hana shi samun damar sayen fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara domin fafatawa da Bola Tinubu
- Bayero Lawal ya bukaci kotu ta bayyana kudin N100m na fom din takara a matsayin haramtacce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wani jigo a jam’iyyar APC kuma mai neman takarar shugaban kasa, Alhaji Bayero Lawal, ya maka jam’iyyarsa a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
Bayero Lawal ya kai oara kotu ne bisa zargin APC da hana shi sayen fom din nuna sha’awa da na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani da aka gudanar kwanakin baya.

Kara karanta wannan
An tono wata doka, Tinubu na iya rasa damar tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa a cikin karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1020/2026, Lawal ya hada da Kwamitin Tantance 'Yan Takarar Shugaban Kasa na APC da kuma Hukumar Zabe (INEC) a matsayin wadanda ake kara.
Ya ce an hana shi fafatawa da Tinubu
Rahotanni sun nuna cewa APC ta amince da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ba tare da an tantance shi ba kafin zaben fidda gwani na 2027, tana mai cewa hakan ya dace da kundin tsarin mulkin jam’iyyar da dokokinta.
Mai magana da yawun APC, Felix Morka, ya bayyana cewa Kwamitin Gudanarwa na Kasa (NWC) ne ya dauki wannan mataki a taronsa na 188 da aka gudanar a ranar 6 ga Mayu, 2026, a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja.
Lawal ya kalubalanci kudin fom
Sai dai a ranar 21 ga Mayu, Lawal, ta hannun lauyansa Basil Kpenkpen, ya shigar da kara yana mai cewa jam’iyyar APC ta hana shi damar sayen fom din nuna sha’awa da na tsayawa takara domin fafatawa da shugaban kasa mai ci.

Kara karanta wannan
Zaben 2027: Takarar Sheikh Pantami a Gombe na tsaka mai wuya, jam'iyyar PDP ta yi bayani
A cikin takardar karar, Lawal ya nemi kotu ta ba shi wasu umarni guda bakwai, ciki har da bayyana kudin da aka sayar fam din APC Naira miliyan 100 a matsayin haramtacce.
Ya kafa hujjar cewa babu wani tanadi a kundin tsarin mulkin APC da ya wajabta biyan irin wannan kudi domin neman takarar shugaban kasa.

Source: Getty Images
Hujjojin da jigon APC ya kafa a kotu
Lawal ya bayyana cewa shi cikakken mamba ne na APC wanda ke biyan dukkan hakkokin jam’iyya, don haka kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya ba shi cikakken 'yancin neman kowace kujera ta zabe, ciki har da ta shugaban kasa.
Ya bukaci kotu ta kare hakkinsa tare da tabbatar da cewa an gudanar da tsarin zaben fidda gwani bisa ka’idojin dimokuradiyya da dokokin jam’iyyar ba.
ADC na so a soke takarar Tinubu
Kun ji cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta yi ikirarin cewa Shugaba Bola Tinubu bai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba.
ADC ta danganta hakan d zargin rashin gabatar da takardun karatunsa na firamare da sakandare ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC
Ta kafa hujja da Sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, wanda ya ce ya haramta wa duk wanda ya gabatar da takardar bogi ga INEC tsayawa takarar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng