Trump Ya Kama Hanyar China, zai Tattauna Batun Iran da Shugaba Jinping

Trump Ya Kama Hanyar China, zai Tattauna Batun Iran da Shugaba Jinping

  • A makon a muke ciki ne shugaban kasar Amurka zai kai ziyara mai muhimmanci zuwa kasar China domin tattauna lamuran da suka shafi duniya
  • A wani bayani da Donald Trump ya yi, ya nuna cewa zai yi doguwar tattaunawa da shugaban China, Xi Jinping game da alakarsa da kasar Iran
  • Tun a kwanakin baya Trump ya tsara zai kai ziyara kasar China amma yakin Amurka/Isra'ila da Iran ya hana shi tafiyar saboda matsalolin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai roƙi Xi Jinping da ya buɗe kofar China ga kamfanonin Amurka yayin da ya nufi Beijing ranar Laraba domin wani muhimmin taro wanda kuma zai taɓo batun yaƙin Iran.

A wata alama da ke nuna yadda Trump ya fi mayar da hankali kan harkokin kasuwanci, shugaban ya dauki manyan 'yan kasuwar Amurka yayin tafiyar.

Kara karanta wannan

Yadda kasar UAE ta rika sakin bama bamai a Iran ta bayan fage

Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump ya shiga jirgi zai tafi China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton AP ya nuna cewa Trump ya kama hanyar China tare da shugaban kamfanin Nvidia, Jensen Huang da shugaban Tesla kuma attajirin duniya, Elon Musk.

Me Trump zai tattauna da China?

Shugaba Donald Trump ya nuna cewa zai nemi hadin kan China domin bunkasa kasuwanci musamman tare da ba 'yan kasuwar Amurka alaka da kasar.

“Zan roƙi shugaba Xi, jagora mai matuƙar daraja, da ya buɗe kofofin China domin waɗannan hazikan mutane su nuna bajintarsu, su kuma taimaka wajen kai Jamhuriyar China zuwa wani mataki mafi girma!”

Trump bayan barinsa Washington zuwa China.

Wasu manyan shugabannin kamfanoni da dama, ciki har da shugaban Apple, Tim Cook za su kasance a Beijing domin wannan ziyara, wadda ita ce ta farko da wani shugaban Amurka zai kai China cikin kusan shekara 10.

Sai dai burin Trump na ƙara bunƙasa kasuwanci zai fuskanci matsalolin siyasa da suka shafi Taiwan da kuma yaƙin Gabas ta Tsakiya, waɗanda suka riga suka jinkirta tafiyar tun a watan Maris, 2026.

Kara karanta wannan

Babban mai goyon bayan Isra'ila ya mutu a Amurka bayan ya yabi Trump kan Iran

Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump ke bankwana da jama'a zai tafi China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun tattaunawa kan Iran

Yayin da yake barin White House, Trump ya ce yana sa ran yin doguwar tattaunawa da Xi kan Iran, wadda ke sayar da yawancin man fetur ɗinta da Amurka ta sanya wa takunkumi ga China.

Ya rage girman sabanin da ke tsakaninsu, inda Al-Jazeera ta ce ya gaya wa ’yan jarida cewa:

“Ba na ganin muna buƙatar taimakon China kan Iran”

Sai dai Beijing na ƙara nuna gajiyawa wajen jiran ganin zaman lafiya ta samu, inda ministan harkokin wajen China ya roƙi takwaransa na Pakistan ranar Talata da ya ƙara ƙoƙarin shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka.

Tafiyar, wacce ita ce ta farko tun bayan da Trump ya ziyarci Beijing a 2017, za ta ƙunshi muhimman tattaunawa da Xi ranar Alhamis da Juma’a, tare da manyan shagulgula da liyafa.

Tsuntsu ya firgita Trump

A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaba Donald Trump ya firgita bayan hango wani tsuntsu na wucewa ta saman shi a fadar White House.

Kara karanta wannan

Yakin Iran da Isra'ila: An 'gano' kasar da tafi cin moriyar rikicin fiye da Amurka

Trump ya dakatar da bayanin da ya ke yana kallon sama, yana gargadi da cewa yanzu haka ana kera jirage marasa matuka masu hadari a duniya.

Hankalin Donald Trump ya tashi ne bayan ganin tsuntsun lura da cewa Amurka na zaman doya da manja da kasashen duniya da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng