Sojojin Iran Sun Yanke Matsaya kan kai Hari Ukraine da ke Yaki da Rasha

Sojojin Iran Sun Yanke Matsaya kan kai Hari Ukraine da ke Yaki da Rasha

  • Iran ta yi ikirarin cewa ta shirya kai hare-hare kan wurare uku a Ukraine amma ta dakatar da shirin bayan Kyiv ta ba da hakuri
  • Wani babban mai bai wa Jagoran Addinin Iran shawara ya ce an dauki matakin ne bayan harin da Ukraine ta kai kan wani jirgin ruwa
  • Rahotanni sun nuna cewa hakan ya biyo bayan Ukraine ta kai hari kan ani jirgin ruwa ne da ke jigilar kayan soja tsakanin Iran da Rasha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran – Iran ta yi ikirarin cewa ta shirya kai hare-hare kan wurare uku a kasar Ukraine, amma daga bisani ta dakatar da shirin bayan gwamnatin Kyiv ta ba da hakuri kan wani hari da aka kai kan jirgin ruwa da ke jigilar kayan soja tsakanin Iran da Rasha.

Kara karanta wannan

Tattaunawa tsakanin Iran da Amurka ta sake tayar da sabon tarnaki bayan ikirarin Trump

Wani babban mai bai wa Jagoran Addinin Iran shawara, Mohsen Rezaei, ne ya bayyana hakan, yana mai cewa Tehran ta canja shawara bayan tattaunawar diflomasiyya da aka yi tsakanin kasashen biyu.

Mojtaba Khamenei na kasar Iran
Mojtaba Khamenei a gefen hagu da jirgin yaki a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jerussalem Post ta rahoto cewa Rezaei ya ce Iran ta shirya mayar da martani ne bayan harin da Ukraine ta kai kan wani jirgin ruwa a Tekun Caspian a ranar 25 ga watan Yulin 2026.

Iran ta soke kai hari Ukraine

A cewar Rezaei:

"Mun shirya kai hari kan wurare uku a Ukraine, amma muka soke shirin bayan Ukraine ta ba da hakuri."

Sai dai rahoton ya nuna cewa Rezaei bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da ikirarin nasa ba, haka kuma bai bayyana wuraren da aka shirya kai harin ba.

Har ila yau, ANI News ta wallafa cewa babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da sahihancin wannan ikirari a bayyane kuma Ukraine ba ta fito ta karryata shi ba.

Yadda rikicin ya lafa

Bayan Iran ta nuna rashin jin dadinta kan harin jirgin ruwan, mukaddashin Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Andrii Sybiha, ya tattauna ta waya da takwaransa na Iran, Abbas Araghchi.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sake kunyata Trump a idon duniya

Rahotanni sun ce yayin tattaunawar, Ukraine ta bayyana cewa harin ba da gangan aka kai shi ba, yayin da Iran ta ce ba ta neman kara rura wutar rikici.

Sybiha ya ce ya bayyana wa Iran cewa dukkan matakan da Ukraine ke dauka suna da nufin kare kasarta daga hare-haren Rasha ne, ba wai kai hari kan jiragen fararen hula ko mutane ba.

shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy
Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine a wajen wani taro. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton ya ce wannan lamari ya zo ne yayin da dangantakar Iran da Ukraine ke ci gaba da tabarbarewa tun bayan da Tehran ta fara bai wa Rasha jiragen yaki marasa matuka a shekarar 2022 tare da ba da lasisin kera su a cikin Rasha.

Maganar trump kan Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa da Iran duk da cewa Tehran ta musanta hakan.

Trump ya ce ya amince da ci gaba da tattaunawar ne bayan bukatar da Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa, Qatar da wasu kasashen yankin suka gabatar.

Sai dai gwamnatin Iran ta musanta cewa akwai wata tattaunawa kai tsaye ko ta kaikaice da Amurka, yayin da Trump ya ce har yanzu yana bai wa Tehran damar cimma yarjejeniya kafin daukar wasu matakai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng