Rashin Imani: Yadda Ƴan Bindiga Suka Kashe Masu Juna 2 da Tarin Mutane a Filato
- Akalla mutane 13 ne aka kashe, ciki har da mata masu juna biyu guda uku, a wani harin dare da aka kai ƙauyen Ngbra Zongo a ƙaramar hukumar Bassa
- A wani harin daban da ya faru a ƙaramar hukumar Barkin Ladi, an rahoto cewa 'yan bindiga sun kashe makalla utane biyar tare da raunata wasu uku
- Al'ummomin da abin ya shafa sun nuna damuwa kan yadda hare-haren ke yawaita, inda suka roki jami'an tsaro da su ƙara kaimi wajen kare rayukansu
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Filato - A ranar Juma'a, akalla mutane 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu, yayin da wasu da dama suka sami raunuka lokacin da mahara suka far wa al'ummar Ngbra Zongo da ke gundumar Kwall a ƙaramar hukumar Bassa ta jihar Filato.
Wani mazaunin yankin, Mista Philip Alanga, ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na dare yayin da mazauna garin ke barci.

Source: Getty Images
Filato: 'Yan bindiga sun yi kisa a Bassa
Philip Alanga ya bayyana wa jaridar Daily Trust cewa:
“Sun shigo cikin garin suka fara harbi. Sun riƙa bi gida-gida suna bude wa mutane wuta babu kakkautawa.”
Wani mazaunin garin, Mista Chigoji Rocku, ya ƙara da cewa uku daga cikin waɗanda aka kashe mata ne masu juna biyu.
Sakataren ƙungiyar raya ƙasar Irigwe (IDA), Mista Danjuma Auta, ya koka kan yadda ake yawan kai wa yankunan Bassa hare-hare, inda ya buƙaci jami'an tsaro da su gaggauta kamo waɗanda ke da hannu a kisan.
Ya kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakai na kare faruwar hare-haren da ake kai wa gruruwan da ke karkashin Bassa,
Kyaftin Polycarp Oteh na rundunar Operation Enduring Peace da kuma SP Alabo Alfred na rundunar 'yan sandan jihar Filato ba su mayar da martani kan wannan hari ba tukunna.

Source: Getty Images
Harin Nding Susut a Barkin Ladi

Kara karanta wannan
Shin da gaske 'yan bindiga sun kashe mutane a wurin jana'iza a Plateau? Gaskiya ta bayyana
Wannan na zuwa ne yayin da Channels TV ta ruwaito cewa 'yan bindiga sun kai farmaki garin Nding Susut da ke gundumar Fan a ƙaramar hukumar Barkin Ladi a ranar Talata.
Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa mutane biyar ne suka rasa rayukansu yayin da wasu uku suka sami raunuka.
Mazauna yankin sun ce maharan sun afka wa garin ne da misalin ƙarfe 8 na dare, inda suka buɗe wa mutanen da ke zaune a wajen gidajensu wuta.
Kakakin ƙungiyar matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya bayyana cewa maharan sun bi ɗaya daga cikin waɗanda suka tsere har suka kashe shi, yana mai bayyana yanayin a matsayin abin damuwa ƙwarai.
Sai rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun riga sun bazama yankunan da aka kai harin domin tabbatar da doka da oda tare da hana sake afkuwar makamancin haka.
'Yan bindiga sun kai hari ana jana'iza
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hari kan masu jana'izar gawarwakin da aka kashe a yankin karamar hukumar Barkin Ladi ta Filato.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun kai hare-hare kusan kauyuka biyar lokaci guda, kuma ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu.
Sakataren kungiyar 'yan kabilar Berom, Rwang Tengwong ya bayyana lamarin a matsayin babban abin tashin hankali.
Asali: Legit.ng
