Abin ya yi muni: Hotuna sun nuna yadda mutane fiye da 15 suka mutu a hanyar Kogi
- Akalla mutane 16 ne suka riga mu gidan gaskiya a safiyar ranar Juma'a sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru a Kogi
- Hatsarin ya raba mutane biyar da lafiyarsu, yayin da mutum guda ɗaya kacal ya tsira ba tare da ko ƙwarzane ba a cikin motar da ke ɗauke da mutane 22
- Hukumar FRSC ta bayyana cewa gajiya da kuma gudu fiye da ƙa'ida ne suka yi sanadin wannan mummunan hatsari da ya salwantar da rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kogi - Akalla fasinjoji 16 ne suka rasa rayukansu a safiyar ranar Juma'a a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ƙauyen Aku, kusa da Osara, da ke kan hanyar Lokoja zuwa Okene a jihar Kogi.
Hatsarin ya afku ne lokacin da wata motar bas nau'in Toyota Hiace, wadda ke tafiya daga Jos na jihar Filato zuwa Legas, ta sauka daga kan titi yayin da take tunkarar wata gada, inda ta faɗa cikin rami.

Source: Twitter
Mummunan hatsari ya afku a jihar Kogi
Kwamandan hukumar kiyaye haɗurra ta FRSC na shiyyar jihar Kogi, Lawal Fagge, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust cewa hatsarin ya faru ne da sanyin safiyar Juma'a.
Lawal Fagge ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa gajiyar da direba ya yi da kuma gudu fiye da ƙa'ida ne suka janyo hatsarin.
Fagge ya bayyana cewa:
“Wani wanda ya tsira ya shaida mana cewa sa’ar da suke tafe, sun gargaɗi direban ya tsaya ya huta na ɗan lokaci lokacin da suka ga alamun gajiya ta yi masa yawa, amma ya ƙi ji, ya ci gaba da tuƙi har sai da ya yi hatsari a dai dai gada.”
Alƙaluman waɗanda abin ya shafa
Motar bas ɗin, wadda aka ƙera don ɗaukar mutane 18, tana maƙare da mutane 22 a lokacin da hatsarin ya faru, inda rahotanni suka ce mutane 16 sun mutu nan take a wurin da abin ya faru.
Hakazalika, an rahoto cewa mutane biyar sun samu munanan raunuka kuma an kai su asibitin Lokoja yayin da mutum daya ne kawai ya tsira daga hatsarin ba tare da wani rauni ba.
Bugu da kari, an ruwaito cewa yawancin waɗanda abin ya shafa maza ne, su 21, yayin da mace ɗaya ce kacal a cikin motar.
Kafar yaɗa labarai ta Zagazola Makama ta bayar da rahoton cewa hatsarin motar mai lamba BUU 17 ZD da ta taso daga Jos ya faru ne da misalin ƙarfe 9:20 na safe.
Kalli hotunan hatsarin a kasa:

Source: Twitter
Gargaɗin hukumar FRSC ga direbobi
Jami'an ceto daga sashin Zariagi na hukumar FRSC sun isa wurin da wuri domin kwashe waɗanda abin ya shafa da kuma kawar da baraguzan motar daga kan hanya.
An ajiye gawarwakin waɗanda suka rasu a ɗakin ajiyar gawa na Ankuri da ke Lokoja, kamar yadda rahoton ya nuna.
Kwamanda Lawal Fagge ya yi kira ga direbobi da su kasance masu kiyaye dokokin tuki a kan titi, su guji gudu fiye da ƙa'ida, sannan su tabbatar sun huta idan sun ji gajiya.
Mutane sun mutu a hanyar jana'iza
A wani labari, mun ruwaito cewa, an tabbatar da cewa hatsarin mota ya kashe mutane shida bayan karo tsakanin motar diban kasa da wata Bas.
Majiyoyi sun tabbatar da mutuwar mutanen wadanda aka ce sun rasa ransu ne yayin da suke dawo wa daga jana'izar wani dan uwansu da ya rasu.
Hukumar FRSC ta tabbatar da cewa hatsarin ya faru sakamakon sakaci da gudun wuce sa'a da direba ya yi, inda mutane 32 suka tsira da raunuka.
Asali: Legit.ng


