
Siyasar Amurka







Sanata Geraldine Thompson ta jihar Florida a ƙasar Amurka ta riga mu gidan gaskiya bayan an mata tiyata domin gyara mata gwiwarta a ƙasar Amurka.

FBI ta cafke Oba Joseph Oloyede, Sarkin Ipetumodu, bisa zargin satar kudaden tallafin COVID-19. Ya samu miliyoyin daloli ta hanyar takardun karya.

Dakatar da ayyukan USAID ya kawo cikas ga rarraba kayan tazarar haihuwa a Bauchi, amma gwamnatin jihar ta ware N50m don tallafawa UNFPA wajen samar da kayayyakin.

A tsawon shekaru, tallafin Amurka ga Najeriya ya fi karkata kan muhimman fannoni kamar lafiya, tsaro, da ci gaban tattalin arziki don magance kalubalen gaggawa

Shugaban Amurka ya samu tirjiya kan kokarin mamaye Gaza da fitar da Falasdinawa daga kasarsu ta asali. Kasashen sun ce Trump bai isa ya kori Falasdinu ba.

'Yan Najeriya da suka zamo bakin haure a Amurka sun ce suna buya a gida domin kaucewa kamun da shugaba Donald Trump ya sa a yi wa bakin haure a kasar.

Kotu a ƙasar Amurka ta yanke wa Sanata Bob Menendez hukuncin zaman gidan kaso na tsawon sheƙaru 11 bayan kama shi da laifin cin hanci da rashawa.

Farashin mai ya fadi bayan Trump ya kafawa Saudiyya da OPEC kahon zuka a kan su rage farashin. Ya kuma yi alkawarin sanya takunkumi kan Rasha da China.

Shugaban Amurka ya dakatar da tallafin lafiya na masu cutar HIV da ake turawa kasashen Afrika da kasashe masu tasowa. Dokar Trump za ta yi tasiri a Najeriya.
Siyasar Amurka
Samu kari