Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Rashi, Tinubu Ya Shiga Jimamin Rashin Dattijo da Ya Mutu
- Shugaba Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwar mahaifin daya daga cikin hadimansa wanda ya rasu bayan fama da jinya
- Tinubu ya ce marigayin ya rayu cikin mutunci, ladabi da hidima, tare da jajanta wa Segun Dada da iyalansa kan wannan babban rashi
- Shugaban ya yabawa gudunmawar marigayin a aikinsa da rayuwar iyali, sannan ya yi addu'ar Allah Ya gafarta masa Ya ba iyalansa hakurin jure rashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar shugaban kasa a Najeriya ta yi babban rashi bayan mutuwar mahaifin hadimin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana matukar alhininsa kan rasuwar Cif Idowu Folorunsho Dada, mahaifin hadiminsa, Olusegun Dada.

Source: Twitter
A cikin sakon ta'aziyyar da aka fitar wanda jaridar The Sun ta samu, Shugaba Tinubu ya mika sakon jajensa ga Segun Dada da daukacin iyalansu.
Tinubu ya yaba da gudummawar marigayi
Tinubu ya ce marigayin mutum ne da ya bar abin koyi na mutunci, ladabi da hidima wanda al'ummomi masu zuwa za su ci gaba da tunawa da shi. Cif Dada ya rasu yana da shekaru 91.
Ya bukace su da su samu kwarin gwiwa daga kyakkyawar rayuwa da kuma gadon alheri da marigayin ya bari.
Shugaban ya ce:
"Ina mika ta'aziyyata ta zuciya ga 'ya'yan Pa Dada da sauran dangin iyalansu bisa rasuwar jagoran iyalinsu.
"Musamman ina jajanta wa Segun a wannan lokaci mai wahala ga iyalinsu, ya dace su sami kwanciyar hankali saboda kyakkyawan suna da hidimar da Cif Dada ya bari."
A cewar Shugaba Tinubu, Cif Dada ya yi fice a lokacin da yake aiki a matsayin tsohon manajan tallace-tallace na kamfanin NEXAN Kablemetal.
Ya ce kwarewarsa, jajircewarsa da rikon amana sun sa abokan aiki da sauran mutane suka girmama shi.
Yabon da Tinubu ya yi ga marigayin
Shugaban ya kuma yabawa marigayin saboda kasancewarsa uba nagari kuma mai tarbiyya wanda ya tabbatar da tarbiyyar yaransa lokacin da ya ke raye.
Ya ce ya dasa kyawawan dabi'u a cikin 'ya'yansa, ciki har da Segun Dada wanda ke aiki a fadar shugaban kasa.
Tinubu ya kuma yabawa jajircewar marigayin ga addinin Kirista da kuma irin kyakkyawar rayuwar iyali da ya gudanar, ya ce gudunmawar da ya bayar abin koyi ce ga sauran al'umma.
A karshe, Shugaban ya yi addu'ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya ba iyalansa da masoyansa hakuri da juriyar wannan babban rashi.
Kwankwaso ya yi jimamin mutuwar mawakin Kwankwasiyya
A baya, an ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana jimaminsa kan rasuwar fitaccen mawakin Kwankwasiyya wanda ya ba da gudummawa.
Kwankwaso ya ce gudunmawar Kosan Waka wajen da yada manufofin tafiyarsu ba za ta taba gushewa ba, yana mai jaddada cewa za a ci gaba da tunawa da shi.
Tsohon gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya sanya shi Aljannatul Firdaus, tare da mika ta'aziyya ga iyalansa da abokansa masu alhini.
Asali: Legit.ng
