Gwamnati Ta Gyara wa Atiku Zancensa kan Zargin Tabarbarewar Tattalin Arziki
- Fadar Shugaban Kasa ta mayar wa Atiku Abubakar martani kan zargin gwamnatin Bola Tinubu da almubazzaranci da tattalin arziki
- Ta ce Atiku ya dogara ne da alkaluman shekarar 2024, ba tare da la'akari da ci gaban tattalin arzikin da aka samu a 2025 da 2026 ba
- Fadar Shugaban Kasa ta kare cire tallafin mai, gyaran haraji da bashin gwamnati, tana mai cewa gyare-gyaren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani ga tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, bayan ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da almubazzaranci da tattalin arziki.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa sukar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya yi ta dogara ne da tsoffin alkaluman shekarar 2024.

Source: Facebook
Arise News ta kawo labarin cewa kalaman Atiku sun dogara da alkaluman ba tare da yin la'akari da sauye-sauyen da aka samu a tattalin arzikin Najeriya a shekarun 2025 da 2026 ba.
Martanin gwamnati ga Atiku
Jaridar Punch ta wallafa cewa Fadar Shugaban Kasa ta ce har yanzu Atiku yana kallon tattalin arziki ne da alkaluman shekarar 2024, alhali tattalin arzikin Najeriya ya samu gagarumar farfadowa tun bayan sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.
Ta ce:
"Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da almubazzaranci wajen tafiyar da kudin kasa, ya kuma yi tambayoyi kan bashin gwamnati, cire tallafin mai da gyaran haraji."
Ta kara da cewa:
"Duk da cewa zarge-zargen nasa ba su dace ba, ya dace a mayar masa martani domin 'yan Najeriya su fahimci hakikanin matsayin tattalin arzikin kasar nan a yau."
Gwamnati ta kare gyare-gyaren tattalin arziki
A cewar sanarwar, darajar GDP na Najeriya da ake aunawa da Dalar Amurka ta karu daga kusan Dala biliyan 253 bayan sauyin tsarin musayar kudi zuwa kusan Dala biliyan 377, wanda ya nuna karin 49%.

Source: Facebook
Haka kuma an shaidawa Atiku Abubakar cewa GDP da ake aunawa da Naira ya karu daga Naira tiriliyan 314 zuwa kusan Naira tiriliyan 530, karin kusan 69%.
Fadar Shugaban Kasa ta ce:
"Tattalin arzikin Najeriya bai tsaya cak a lokacin da ya fi fuskantar kalubale ba."
Ta kuma kare bashin da gwamnati ke ci, tana mai cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne karfin tattalin arziki da kudaden shiga, ba yawan bashin kadai ba.
Sakon Atiku ga yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya buƙaci matasan Najeriya su guji sayar da ƙuri'unsu, yana mai cewa hakan zai lalata makomarsu da hana samun shugabanci nagari da za su kawo sauyi.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar wanda ke takarar 2027 a jam'iyyar ADC ya ce matasa su ƙi karɓar kuɗi, shinkafa ko wasu kyaututtuka domin zaɓen shugabannin da ba su cancanta ba.
Dan takarar ADC ya kuma buƙaci matasa su yi rajistar zaɓe, su kare ƙuri'unsu tare da gujewa rikicin siyasa da rarrabuwar kawuna a yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a farkon 2027.
Asali: Legit.ng


