Amurka Ta Lissafa Najeriya da Wasu Kasashen Afrika dake Fuskantar Barazanar Tsaro

Amurka Ta Lissafa Najeriya da Wasu Kasashen Afrika dake Fuskantar Barazanar Tsaro

  • Amurka ta ce fataucin miyagun kwayoyi da safarar mutane sun karu fiye da sau shida a Afirka cikin shekaru biyu
  • Najeriya na cikin kasashen da za su amfana da sabon shirin Amurka na bunkasa manyan ayyukan more rayuwa masu jawo masu zuba jari
  • AFRICOM ta ce hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka ne kadai zai iya dakile sabbin barazanar tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Gwamnatin Amurka ta yi gargadin cewa Najeriya da sauran kasashen Afirka na fuskantar karuwar barazanar tsaro fiye da sau shida cikin shekaru biyu da suka gabata, sakamakon karuwar safarar miyagun kwayoyi da kuma cinikin mutane a nahiyar.

Haka kuma, Amurka ta bayyana Najeriya, Kenya da Cote d'Ivoire a matsayin manyan kasashen da za su ci gajiyar sabon shirinta na taimakawa gwamnatocin Afirka wajen tsara manyan ayyukan more rayuwa da za su iya jawo jarin kamfanonin Amurka.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta zagaye, ta sayo makaman kariya na miliyoyin Dala a China

Amurka ta gargadi Najeriya kan karuwar matsalar tsaro
Shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

AFRICOM ta bayyana sabbin barazanar tsaro

Daraktan sashen dabarun sufuri na rundunar AFRICOM ta Amurka, Birgediya Janar Paul G. Filcek, ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai ta yanar gizo da ya yi da 'yan jaridar Afirka a gefen taron ALCS2026 in ji rahoton Vanguard.

An gudanar da taron ne tare da Ma'aikatar Tsaron Habasha, inda wakilai daga kasashe 39 na Afirka da kamfanoni masu zaman kansu 27 suka halarta domin tattauna hanyoyin inganta tsaro da hadin gwiwa.

Filcek ya ce nahiyar Afirka na fuskantar sabbin kalubalen tsaro da suka hada da safarar mutane da kuma fataucin miyagun kwayoyi, wanda ya ce ya karu fiye da sau shida idan aka kwatanta da shekaru biyu da suka gabata.

Yadda za a shawo kan matsalolin

Ya ce shawo kan irin wadannan matsaloli na bukatar hadin gwiwa tsakanin kasashen Afirka, ingantaccen tsarin sadarwa da kuma damar jigilar jami'an tsaro, kayan aiki da kayayyaki cikin gaggawa zuwa wuraren da ake bukata.

Kara karanta wannan

Najeriya ta jawo wa kanta, Amurka ta shirya dakile duk wani tallafi ga ƙasar

A cewarsa, wannan ne karo na farko da aka hada batutuwan dabarun sufuri da sadarwa cikin taro guda, yana mai cewa hakan zai kara karfin kasashen Afirka wajen tinkarar matsalolin tsaro na zamani.

Najeriya ta shiga shirin jawo jarin Amurka

A nasa bangaren, Mataimakin Sakataren Kasuwancin Amurka mai kula da Gabas ta Tsakiya da Afirka, Mark Mitchell, ya bayyana cewa Ma'aikatar Kasuwanci da Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka na gudanar da wani sabon shiri mai suna TABI.

Ya ce manufar shirin ita ce taimaka wa gwamnatocin Afirka wajen tsara manyan ayyukan more rayuwa da za su kasance masu jan hankalin masu zuba jari daga Amurka tare da samar da amfani ga al'ummomin kasashen.

Amurka ta gargadi Najeriya da wasu kasashen Afrika kan matsalar tsaro.
An gudanar da taron #ALCS2026 tsakanin Amurka da kasashe Afrika 40 a Addis Ababa. Hoto: @AfricaMediaHub
Source: Twitter

Mitchell ya bayyana cewa Najeriya, Kenya da Cote d'Ivoire na daga cikin kasashen da Amurka ke aiki tare da su wajen inganta yanayin kasuwanci, tsarin gudanar da bayanai da kuma hada-hadar zuba jari.

Jaridar Tribune ta rahoto ya ce manufar shirin ita ce bai wa kasashen Afirka damar cin gashin kansu ta fuskar ci gaba, maimakon dogaro da tallafi daga kasashen waje.

Mitchell ya kara da cewa hadin gwiwar da Amurka ke yi da Najeriya da sauran kasashen ya nuna kudurinta na samar da kasuwanni masu gaskiya, gasa da kuma dokoki da ke kare ikon kasashe tare da inganta kirkire-kirkire da ci gaban tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Tsadar fetur: Yan Najeriya na fuskantar sabuwar barazana ta tsadar abinci

Zarrar sojojin Najeriya a Afrika

A wani labarin, mun ruwaito cewa, rundunar Sojin Najeriya ta samu lambar yabo daga African Security Watch a matsayin mafi ƙwarewa a Afirka wajen yaƙi da ta'addanci a 2025.

Shugaban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya sadaukar da lambar yabon ga sojojin da suka rasa rayukansu da iyalansu.

Kungiyar African Security Watch ta ce nasarorin rundunar sun samo asali ne daga haɗin gwiwa, tattara bayanan sirri da inganta horon sojoji

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com