An Cimma Matsaya da Hamas, Trump zai Fatattaki Isra'ila a Gaza

An Cimma Matsaya da Hamas, Trump zai Fatattaki Isra'ila a Gaza

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sanar da abin da ya kira yarjejeniya ta tarihi domin kwance damarar Hamas da sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Zirin Gaza
  • Trump ya ce matakin zai buɗe hanyar janye sojojin Isra'ila daga Gaza tare da kafa sabuwar gwamnatin Falasɗinawa da za ta jagoranci yankin
  • Sai dai Hamas ba ta tabbatar da yarjejeniyar ba, yayin da ƙungiyar Islamic Jihad ta Falasɗinu ta ce rahotannin da ke cewa an cimma irin wannan yarjejeniya ba su da inganci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington DC, Amurka – Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya sanar da cewa an cimma wata yarjejeniya da ya bayyana a matsayin ta tarihi domin kwance damarar Hamas a Gaza.

Trump ya ce yarjejeniyar za ta zama wani babban mataki na samar da zaman lafiya mai ɗorewa da kuma tabbatar da tsaro a yankin bayan watanni ana tattaunawa kan shirinsa na kawo ƙarshen yaƙin Gaza.

Kara karanta wannan

An ragargaji tankar gas din Amurka tana tafiya a teku, ta kama da wuta

Donald Trump a wajen taro
Shugaba Donald Trump yana yi wa 'yan Amurka jawabi. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Trump ya yi bayani kan yarjejeniyar

CNN ta rahoto cewa Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa da kan shi yayin da ake kokarin samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.

A cewar Trump:

"Yau Hukumar Board of Peace ta cimma yarjejeniya ta tarihi domin kwance damarar Hamas da duk sauran ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a Gaza."

Wani jami'in BoP ya ce a ƙarƙashin yarjejeniyar, Hamas da sauran ƙungiyoyi za su miƙa makamansu ga kwamitin da aka kafa, inda za a fara da makaman 'yan sanda kafin daga bisani a karɓi makaman daidaikun mutane.

Jami'in ya ce idan aka aiwatar da yarjejeniyar, za a kafa gwamnatin riƙon ƙwarya ta ƙwararru a Gaza, yayin da Hamas za ta janye daga shugabanci da harkokin mulkin yankin.

Hamas ba ta magantu ba

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Hamas ba ta fitar da wata sanarwa da ke tabbatar da cimma yarjejeniyar ba.

Kara karanta wannan

Iran ta tsokano Trump, ya sha alwashi bayan an shammaci Amurka

Haka kuma ƙungiyar Palestinian Islamic Jihad Movement ta bayyana cewa rahotannin da ke cewa an cimma yarjejeniya kan kwance damarar ƙungiyoyin ba su da inganci.

Sai dai jami'an Amurka sun ce Isra'ila ta kasance cikin tattaunawar tun daga farko, duk da cewa gwamnatin Isra'ila na ci gaba da nuna shakku kan ko Hamas za ta cika alƙawarin miƙa makamanta.

Shugaba Donald Trump
Lokacin da Donald Trump zai tafi China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Yadda za a aiwatar da shirin

Rahoton BBC ya nuna cewa Donald Trump ya bayyana cewa za a aiwatar da yarjejeniyar ne a matakai daban-daban.

Ya ce yayin da ake kwance damarar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, sojojin Isra'ila za su fara ficewa daga Gaza, sannan wata rundunar tsaron ƙasa da ƙasa tare da sabuwar rundunar 'yan sandan Falasɗinu za su karɓi ragamar tsaro.

Rahotanni sun kuma bayyana cewa birnin Alkahira na Masar zai karɓi bakuncin wata ganawa tsakanin masu shiga tsakani daga Masar, Amurka, Qatar da Turkiyya domin tabbatar da cewa dukkan ɓangarorin sun cika sharuɗan yarjejeniyar.

Iran ta kai hari kan Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta yi iƙirarin cewa ta kai hari da makamai masu linzami kan jiragen sojin Amurka a filin jirgin Aqaba da ke Jordan.

Kara karanta wannan

Yadda Iran ta zagaye, ta sayo makaman kariya na miliyoyin Dala a China

IRGC ta ce harin ya janyo mummunar ɓarna ga wasu jiragen sojin Amurka, tare da cewa ta samu bayanan sirri daga wasu mutane a Jordan.

Sai dai rundunar CENTCOM ta Amurka ta ce ta ci gaba da kai hare-hare kan wasu wuraren sojin Iran domin rage barazanar da ke fuskantar zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng