Sheikh Ahmad Gumi Ya Fadi Matsayarsa kan Shigar Malamai Siyasa a Najeriya

Sheikh Ahmad Gumi Ya Fadi Matsayarsa kan Shigar Malamai Siyasa a Najeriya

  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce babu laifi idan malaman addini sun shiga siyasa domin ba da gudunmawarsu wajen shugabanci
  • Malamin ya bayyana cewa malamin da ya shiga siyasa ya fi wanda ke zama yana yi wa 'yan siyasa addu'a a kan buzu kawai
  • Kalaman nasa sun zo ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan takarar tsohon minista Isa Ali Pantami da wasu malamai a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kaduna – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana ra'ayinsa kan muhawarar da ake yi game da ko ya dace malamai su shiga siyasa ko kuma su tsaya kan wa'azi da koyar da addini.

Gumi ya ce babu wani laifi idan malamin addini ya shiga siyasa domin bayar da gudunmawarsa wajen gyaran al'umma da shugabanci.

Kara karanta wannan

ADC ta bukaci Tinubu ya ceto daliban Borno kamar na Oyo

Sheikh Ahmad Gumi
Sheikh Ahmad Gumi a jihar Kaduna. Hoto: Salisu Web Master
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa kalaman malamin sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan shigar wasu fitattun malaman Musulunci siyasa gabanin babban zaben shekarar 2027.

Gumi ya bayyana matsayarsa

A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, Sheikh Gumi ya ce malamin da ya shiga siyasa ya fi wanda ke zama yana yi wa 'yan siyasa addu'a daga gefe.

Sheikh Ahmad Gumi ya rubuta cewa:

"Malamin da ya shiga siyasa a ka yi kwaramniyar siyasar da shi ya fi Malamin da ya zauna kan buzu yana wa 'yan siyasa addu'a."

Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyi daban-daban game da rubutun da Sheikh Ahmad Gumi ya yi, inda wasu suke goyon bayan shi, wasu kuma suke nuna suna da ja.

Pantami ya tayar da muhawara

Muhawarar ta sake daukar zafi ne bayan tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, ya fito takarar gwamnan jihar Gombe a karkashin jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

INEC ta yi fatali da sanya sojoji a tsarin zaben Najeriya, an ji dalili

Masu adawa da shigar malamai siyasa na cewa siyasa cike take da zage-zage, rarrabuwar kawuna da batanci, wanda ka iya rage mutunci da kima da malaman addini ke da ita a idon al'umma.

Sheikh Pantami a wajen taron PDP
Lokacin da PDP ta tsayar da Sheikh Isa Ali Pantami takara. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

Sai dai masu goyon bayan hakan suna ganin ba za a iya kawo sauyi daga waje kawai ba, don haka ya dace malamai masu ilimi da nagarta su shiga siyasa idan suna da burin yi wa al'umma hidima.

PDP ta tabbatar da takarar Pantami

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta daura bayanan takarar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, a shafin hukumar zabe ta kasa (INEC).

Kungiyar Pantamiyya Movement ta ce an kammala loda bayanan Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami a ranar 26 ga watan Yuli domin takarar gwamnan jihar Gombe a zaben shekarar 2027.

Kungiyar ta kara da cewa Pantami ya zama dan takarar gwamna ba tare da hamayya ba, bayan sauran masu neman takarar sun kasa samun takardar tantancewa daga kwamitin gudanarwa na jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng