Yakin Iran: An Samu Baraka, Trump Ya Sauke Shugaban Sojin Ruwan Amurka

Yakin Iran: An Samu Baraka, Trump Ya Sauke Shugaban Sojin Ruwan Amurka

  • Gwamnatin Donald Trump ta sauke shugaban rundunar sojin ruwan Amurka, John Phelan yayin da ake cigaba da takaddama da Iran
  • Rahotanni sun nuna cewa hakan ya biyo bayan nazari da shugaba Trump ya yi, inda ya ke ganin rundunar na bukatar sabon shugabanci
  • White House ta yi magana a kan shi, inda aka tabbatar da cewa zai ajiye aikin shi nan take kafin daga baya a maye gurbinsa da wani

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - An sauke Shugaban rundunar sojan ruwan Amurka, John Phelan, daga mukaminsa a ranar Laraba, 22 ga watan Afrilun 2026.

Ba a bayyana dalilai karara kan sanadin sauke shi ba, sai dai an haska cewa kasar na bukatar sabon hannu a rundunar sojin ruwa a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Yaki da ta'addanci: An hango sojojin Najeriya a Amurka, ana masu horo na musamman

John Phelan da Donald Trump
Donald Trump a hagu, John Phelan a gefen dama. Hoto: @SECNAV|Getty Images
Source: Twitter

Wasu majiyoyi shida masu masaniya kan lamarin ne suka shaida wa CNN, a yayin da rikici ke kara tsananta tsakaninsa da inistan yaki, Pete Hegseth, kan yadda yake aiwatar da sauye-sauyen sarrafa jiragen ruwa.

An kori Shugaban sojin ruwan Amurka

Mai magana da yawun Pentagon, Sean Parnell, ya bayyana cewa Phelan zai bar mukaminsa “nan take,” wani mataki da ya zo ba zato ba tsammani.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar ruwan Amurka ke aiwatar da takunkumi kan tashoshin jiragen ruwa na Iran yayin tsagaita wuta a yakin.

A cewar wasu majiyoyi, Hegseth ya tattauna da Trump sannan ya sanar da Phelan cewa dole ne ya yi murabus ko a kore shi daga mukaminsa.

“Shugaba Trump da minista Hegseth sun amince cewa ana bukatar sabon shugabanci a rundunar ruwa,”

In ji wani babban jami’in gwamnati

Tambayoyin da aka jefa wa Donald Trump

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Za a gurfanar da ministan Buhari, malamin Musulunci da wasu a kotu

Rundunar ruwan ta mika tambayoyi game da ficewar Phelan ga ofishin Ministan yaki, wanda bai bayar da amsa nan take ba. Fadar White House ta kuma nuna sanarwar da Parnell ya fitar.

“A madadin ministan yaki da mataimakinsa, muna godiya ga Phelan bisa hidimarsa ga ma’aikatar da rundunar ruwan Amurka,”

In ji Parnell a wani sako da ya wallafa a kafar X.

“Muna masa fatan alheri a gaba. Mataimakin sakatare, Hung Cao, zai zama mukaddashin sakataren rundunar ruwa.”

Sanarwar ta zo a wani lokaci mai matukar muhimmanci, inda rundunar ruwan ke taka rawa wajen hana jiragen Iran wucewa ta mashigar Hormuz.

Pete Hegseth a wai taro a Amurka
Ministan yaki, Pete Hegseth na bayani kan yakin Amurka da Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sabani tsakanin jami'an Amurka

Majiyoyi da dama sun ce an dade ana samun sabani tsakanin Phelan da Hegseth, wanda ke ganin Phelan yana jinkirta aiwatar da sauye-sauyen gina jiragen ruwa.

Wasu rahotanni sun kara a cewa Hegseth bai ji dadin yadda Phelan ke tuntubar Trump kai tsaye ba, wanda ya dauka a matsayin kokarin kauce masa.

Amurka na horas da sojojin Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Amurka, karkashin Shugaba Donald Trump tana ba wasu dakarun sojojin saman Najeriya horo.

Kara karanta wannan

Rasha ta yi tone tone, an ji yadda kasar Musulunci ta Iran ta fada tarkon Amurka

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da cewa ana ba jami'an horo ne kan yadda za su kula da marasa lafiya, musamman ceto sojoji ta sama a fagen fama.

Da zarar sojojin sun kammala samun horo za su dawo gida Najeriya domin cigaba da amfani da ilimin da suka koya wajen yaki da ta'addanci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng