Jirgin Sama Ya Yi Mummunan Hatsari, Dukkan Fasinjojin da Ya Dauko Sun Mutu a Peru
- Akalla mutum 13 sun mutu bayan wani ƙaramin jirgin sama da ke ɗauke da masu yawon buɗe ido ya yi hatsari kusa da wurin tarihi na Nazca Lines
- 'Yan sanda sun ce jirgin ya faɗi jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin Pisco, yayin da hukumomi suka tabbatar babu wanda ya tsira
- Hukumomin Peru sun fara bincike kan musabbabin hatsarin, wanda ya sake tayar da hankali bayan makamantan haɗurra da suka faru a shekarun baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida
Peru - Akalla mutum 13 sun rasa rayukansu bayan wani ƙaramin jirgin sama mai ɗauke da masu yawon buɗe ido ya yi hatsari a kudancin ƙasar Peru, yayin da yake kan hanyarsa ta kai fasinjoji kallon shahararren wurin tarihi na Nazca Lines.
'Yan sandan ƙasar sun tabbatar da cewa fasinjoji 11 da ma'aikatan jirgin biyu ne suka mutu a hatsarin, wanda ya faru jim kaɗan bayan tashin jirgin daga filin jirgin sama na Pisco, mai nisan kusan kilomita 240 daga babban birnin ƙasar, Lima.

Source: Getty Images
Babu wanda ya tsira daga hatsarin
Babban jami'in 'yan sanda, Jorge Andrade, ya ce tsananin hatsarin ya sa babu wanda ya tsira da ransa, in ji rahoton The Guardian.
Ya bayyana cewa jami'an ceto sun fara gano gawarwaki huɗu a wurin da jirgin ya faɗi, yayin da ake ci gaba da aikin ceto da bincike.
Har zuwa lokacin fitar da wannan rahoto, hukumomi ba su bayyana sunayen waɗanda suka mutu ba, kuma ba a san musabbabin hatsarin ba.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Peru ta ce ta fara bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin.
Wurin da ya shahara da masu yawon buɗe ido
Jirgin ya taso ne daga filin jirgin sama na Pisco, wanda ke karɓar ƙananan jiragen da ke jigilar masu yawon buɗe ido zuwa Nazca Lines.
Nazca Lines wani shahararren wurin tarihi ne da Hukumar UNESCO ta ayyana a matsayin kayan tarihi na duniya.
Wurin ya ƙunshi manyan zane-zane da aka sassaka a cikin hamadar ƙasar Peru tsakanin shekara ta 500 kafin haihuwar Annabi Isa zuwa shekara ta 500 bayan haihuwarsa.
Waɗannan zane-zane, waɗanda yawancinsu ke ɗauke da siffofin dabbobi, ana iya ganinsu yadda ya kamata ne daga sama ko kuma daga wasu wuraren kallo da aka tanada.

Source: Getty Images
Ba shi ne hatsari na farko ba
Rahoton DW ya nuna cewa wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan hatsari ya auku a yankin Nazca Lines ba.
A shekarar 2022, wani jirgin yawon buɗe ido ya yi hatsari a yankin, inda mutum bakwai suka mutu, ciki har da 'yan ƙasar Chile biyu da 'yan ƙasar Netherlands uku.
Haka kuma, a shekarar 2010, wani makamancin hatsarin ya yi sanadin mutuwar masu yawon buɗe ido huɗu daga Birtaniya da kuma ma'aikatan jirgin biyu 'yan ƙasar Peru.
Sabon hatsarin ya sake tayar da hankalin jama'a kan matakan tsaro da ake bi wajen jigilar masu yawon buɗe ido zuwa ɗaya daga cikin shahararrun wuraren tarihi na duniya.
Asali: Legit.ng

