Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya koma gida cike da jin kunya lokacin da masu sauya sheka 4000 daga jam’iyyar PDP suka ci bayyana a wani gangami kamar yadda aka sanar da farko a karamar hukumar Birnin Kudu.
A yau aka za a fara sauraron shari’an Maryam Sanda, matar da yan sanda suka zarga da kashe mijinta, Bilyamin Bello. Ana sanya ran yan sanda zasu kira shaidansu na farko a gaban kotu domin bayar da shaidan abunda ya sani.
Soyayya gamuwar jini, inji masu hikimar zance, hakan ce ta faru a lokacin da wata matashiya mai suna Maryam yar shekara 17 tayi tattaki tun daga kasar nijar zuwa Najeriya kawai saboda ta hada ido da shahararren mawaki M. Shareef.
Kamfanin dillancin Najeriya ta tattaro cewa wasu yan bindiga ne suka yi garkuwa dayayan dan majalisan, Muhammad Yahaya da yayansa Junaidu Yahaya a ranar 22 ga watan Janairu a gidansu dake kauyen Gora, karamar hukumar Maradun.
Rahotanni sun kawo cewa Sanata Biodun Olujimi ta karyata rade-radin dake yawo a kaffin watsa labarai na cewa ta sanya daya daga cikin hadiminta ya mari wani ma’aikacin majalisar tarayya, inda shi kuma ya rama a kanta.
An tattaro cewa yan uwan biyu sun karbi Musulunci ne bayan yayrsu mai suna Aishat Obi ta rigada ta karbi Musulunci. NAIJ.com ta ci karo ne da labarin bayan yar uwar tasu wacce ta kasance Musulma ta yada a shafin Facebook.
Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun fara shawagi a jihar Kano domin tabbatar da tsaro a jihar. Hakan ya biyo bayan ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke shirin kaiwa jihar a ranar Talata.
'Yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya sun yi Allah wadai da kalaman babban malamin nan na addinin Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Gumi da ya yi akan Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyya, Ambasada Muhammad Sani Yunusa.
Rahotanni sun kawo cewa kungiyar yan uwa Musulmi mabiya mazhabar Shi’a na ci gaba da zaman dirshan a babban birnin tarayya Abuja. Kamar yadda kuka sani suna gudanar da wannan zama ne domin ganin gwamnatin tarayya ta saki Jagoransu
Aisha Musa
Samu kari