Lokaci Ya Yi: Kwamishina a Adamawa Ya Rasu, Gwamna Fintiti Ya Yi Ta'aziyya
- Mutuwa ta dauki daya daga cikin kwamishinonin jihar Adamawa bayan da kwamishinan noma na jihar, Farfesa David Jatau, ya yi bankwana da duniya
- Farfesa David Jatau ya rasu ne bayan ya yi jinyar rashin lafiya a Abuja, inda daga karshe ya ce ga garinku nan a wani asibiti
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya aika da sakon ta'aziyyarsa kan rasuwar kwamishinan wanda ya bayyana a matsayin jajirtaccen mutum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Adamawa - Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya nuna juyayi kan rasuwar kwamishinan noma na jihar, Farfesa David Jatau.
Marigayi kwamishinan dai ya rigamu gidan gaskiya ne a Abuja bayan ya yi fama da gajeruwar rashin lafiya, a ranar Juma'a, 26 ga watan Yunin 2026.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou ya fitar ranar Asabar, 27 ga watan Yunin 2026 wadda aka sanya a shafin X.

Kara karanta wannan
2027: Ana zargin goyon bayan Sheikh Pantami ya jefa kamfanin Gombawa Motors a matsala
Gwamna Fintiri ya yabawa marigayin
Gwamnan ya bayyana marigayi kwamishinan a matsayin fitaccen masani kuma bawan gwamnati mai sadaukarwa, wanda gudunmawar da ya bayar ga haɓakar ɓangaren noma na jihar Adamawa ta kasance mai babban daraja.
Ya lura cewa Farfesa David Jatau ya taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da manufofin da aka tsara domin inganta wadatar abinci, tallafawa manoma, da kuma ƙarfafa matsayin jihar a matsayin babbar cibiyar ayyukan noma.
Ya ce marigayin ya sadaukar da kansa wajen hidima
Gwamna Ahmadu Fntiri ya ce marigayi kwamishinan ya yi aiki cikin aminci, mutunci, da sadaukarwa, inda ya kawo iliminsa cikin aikin gwamnati kuma ya bar tarihi na ƙwazo da jajircewa a fannin shugabanci.
Ya mika ta'aziyyarsa ga iyalai da aka yi wa rashi, ma'aikatar noma da kuma mutanen jihar Adamawa baki ɗaya, inda ya yi addu'ar Allah ya jikan ran Farfesa Jatau kuma ya ba wa dukkan waɗanda ke jimamin wannan rashi juriya.
“Farfesa Jatau mutum ne mai basira, mutunci, da kuma son hidima. Ya kawo tarin iliminsa zuwa cikin gwamnati kuma ya yi amfani da shi cikin ƙwazo domin haɓakar ɓangaren nomanmu da kuma jin daɗin mutanenmu."
“A madadin gwamnati da mutanen jihar Adamawa, ina miƙa ta'aziyya ga iyalansa na kusa, abokan aikinsa, ma'aikatar noma, da dukkan waɗanda ya hidimarsa ta yi amfani a rayuwarsu "
- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

Source: Twitter
Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba wa ransa hutun dindindin na har abada, sannan ya ba wa iyalansa, abokan aikinsa, da daukacin jihar juriyar jure wannan babban rashi.
Fintiri ya ba Boss Mustapha mukami
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya amince da nadin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, a matsayin wakilin jihar.
Boss Mustapha zai wakilci Adamawa ne a kwamitin amintattu na asusun tsaron Arewacin Najeriya, wanda aka kafa domin tallafawa kokarin inganta tsaro a yankin.
Asusun na da manufar tallafawa tattara bayanan sirri, samar da kayan aiki da kuma bunkasa hadin gwiwa tsakanin jihohin Arewa.
Asali: Legit.ng
