Mabiya Shi’a na ci gaba da zaman dirshan a Abuja don ganin an saki Zakzaky (hotuna)
Rahotanni sun kawo cewa kungiyar yan uwa Musulmi mabiya mazhabar Shi’a na ci gaba da zaman dirshan a babban birnin tarayya Abuja.
Kamar yadda kuka sani suna gudanar da wannan zama ne domin ganin gwamnatin tarayya ta saki shugabansu, Sheik Ibrahim El-Zakzaky wanda ke tsare.
Yan shi’an basu saduda ba duk da artabu da ake sha da su wajen hana su shiga harabar majalisa, inda suka sha fafatawa da yan sanda harma jami’an tsaron suka yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa su.
Zaku tuna cewa sama da shekaru biyu kenan bayan hukumar DSS ta tsare shugaban akidar Shi’a, Ibrahim Zakzaky, bayan wani rikici da ya faru ranan 12 ga watan Disamba 2015 inda akayi asaran rayuka da dama.
KU KARANTA KUMA: Falana ya shawarci gwamnatin tarayya da ta saki El-Zakzaky da matarsa bayan ta tsare su ba bisa doka ba
A yan makonni da suka gabata ne, Sheik Ibrahim Zakzaky ya bayyana kuma yayi hira da manema labarai karo na farko tun lokacin da hukumar ta tsare sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng