'Yan Najeriya mazauna Saudiyya sun yi Allah wadai da kalaman Sheik Ahmad Gumi

'Yan Najeriya mazauna Saudiyya sun yi Allah wadai da kalaman Sheik Ahmad Gumi

'Yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya sun yi Allah wadai da kalaman babban malamin nan na Musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Gumi akan Ambasadan Najeriya a kasar Saudiyya, Ambasada Muhammad Sani Yunusa.

A kwanan nan ne Ahmad Abubakar Gumi ya kira Ambasadan mai Ofis a birnin Jeddah, ta wayar salula inda yake kalubalantar sa akan hana wata mata mazauniya Saudiyya daukan hoton fasfo na tafiya da Nikabi. Ambasadan ya ce ka'idar aiki ba'a daukan hoton fasfo na tafiye tafiye da Nikabi, dole sai an cire, wanda babu kasar da za ta baiwa mace bisa da Nikabi a fiskarta.

Alhaji Isa Muhammad Hadejia shine shugaban Yan Naijeriya Mazauna kasar saudiyya, kuma ya mana Bayanin cewa Bude fuska ba haramun bane a musulunci domin akwai Hadisin da yake cewa mace duk jikinta al aurace banda fuskarta da tafukanta.

Dan haka bai kamata ace babban Malami kamar Dakta Ahmad Gumi zaiyi magana har da ta da jijiyar wuya kan matar da tazo yin fasfo wanda a ka'ida sai ta cire Nikabi sannan a dauketa Hoto, kuma koda ma an dauketa da Nikabi babu kasar da zata bata Visa a duniya.

KU KARANTA KUMA: Ku kama sannan ku hukunta duk wanda aka samu da makamai ba bisa ka’ida ba – Buhari ga hukumomin tsaro

Shafin Rariya ta rahoto inda, Shugaba Isa Hadejia yace Ambasada Muhammad Sani Yunusa yakawo gagarumar nasara a wajen samawa 'yan Naijeriya 'yanci a kasar saudiyya, da farko yace ya bada dama ga duk wani dan Najeriya ya shiga inda ya keso a ofishin Consulate domin gidansa ne, duk dan Najeriya da ya bukaci fasfo zai samu a kwana biyu sabanin a baya ba haka bane, ya dawo da mutuncin 'yan Najeriya a kasar Saudia, to ta yaya Sheikh Gumi zai kira ambasada ta waya, yana cin mutuncin sa akan abun da ba yi da sani ko ilimi a kansa? Me yasa Dr. Gumi yake son dole sai an dauki Hoton mace mai yin fasfo da Nikabi a fuskarta? Shin haka akeyi a Najeriya daukan hoton masu yin fasfo da Nikabi ko kuma kawai yayi wannan ne dan son zuciyarsa?

Wannan tambayoyi ne na musamman wanda ake son Dakta Gumi ya bada amsar su, Inji shugaban 'yan Najeriya mazauna kasar Saudiyya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng