Dakarun Sojoji Sun Farmaki 'Yan Ta'addan Lakurawa a Kebbi, an Kashe Miyagu
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'addan Lakurawa a jihar Kebbi
- Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Lakurawa bayan wani dauki ba dadi da aka yi
- Hakazalika, dakarun sojojin sun samu nasarar kwato makamai masu tarin yawa daga hannun hatsabiban 'yan ta'addan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yammasun kashe mutane biyu da ake zargi 'yan ta'addan Lakurawa ne a jihar Kebbi.
Dakarun sojojin sun kuma sun ƙwato makamai da harsashi yayin wani samame da suka kai a yankin Sabarumawa da ke jihar Kebbi.

Source: Twitter
Jami'in Yaɗa labarai na rundunar, Laftanal Kanal Aliyu Danja, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan
Sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta shigo Arewacin Najeriya? 'Yan sanda sun gano gaskiya
Sojoji sun dana tarko ga 'yan ta'adda
Samamen, wanda aka gudanar ranar Asabar, 27 ga watan Yunin 2026, ya biyo bayan bayanan sirri ne da suka nuna cewa 'yan ta'addan suna shirin kai hari ga al'ummar Sabarumawa.
Lafatanal Kanal Aliyu Danja ya ce dakarun sojojin sun yi hanzarin tashi zuwa yankin inda suka kafa tarkon kwantan ɓauna na dabarun yaƙi a kan hanyar da ake zargin 'yan ta'addan za su bi.
“Nasarar samamen ta biyo bayan ingantattun bayanan sirri ne da suka nuna cewa 'yan ta'addan suna shirin kai hari a garin Sabarumawa."
“Sakamakon yin gaggawar aiki da bayanin, dakarun sojoji sun tashi zuwa yankin kuma suka kafa tarkon kwantan ɓauna kan hanyar da ake zargin 'yan ta'addan za su fito da nufin ruguza harin da suka yi shirin kaiwa."
- Laftanal Kanal Aliyu Danja
An yi arangama da 'yan ta'addan Lakurawa
Laftanal Kanal Aliyu Danja ya ce dakarun sun fafata da 'yan ta'addan yayin da suka kusanci wurin da aka kafa kwantan ɓaunar.

Kara karanta wannan
'Yaran jagoran 'yan bindigan da suka sace Janar sun sake sabon ta'addanci a Katsina
“Yayin da 'yan ta'addan suka kusanci wurin kwantan ɓaunar, dakarun sun fafata da su da gagarumin ƙarfin wuta, lamarin da ya kai ga musayar wuta mai tsanani."
"Kwarewar yaƙi mafi girma na dakarun sojojin ya tilasta wa 'yan ta'addan tarwatsewa cikin rudani, inda aka kashe 'yan ta'adda guda biyu, yayin da sauran mambobin suka tsere zuwa cikin dajin da ke kewaye da yankin."
- Laftanal Kanal Aliyu Danja

Source: Original
Sojoji sun kwato makamai
Ya ce dakarun sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, rumbun adana harsashi na AK-47 guda biyu, harsasai guda 143, da kuma babur guda ɗaya daga wurin da lamarin ya faru.
Laftanal Kanal Aliyu Danja ya sake jaddada sadaukarwar dakarun sojoji wajen ci gaba da kai hare-hare kan gungun 'yan ta'adda da sauran miyagu da ke aiki a faɗin Arewa maso Yamma.
Sojoji sun ceto mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun ceto mutane takwas da aka yi garkuwa da su daga dajin Pandam da ke karamar hukumar Qua’an Pan a jihar Plateau.
Sojoji sun yi arangama da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne, inda aka yi musayar wuta bayan samun sahihan bayanai kan ayyukansu.
Rundunar sojoji ta bayyana cewa dukkan wadanda aka ceto suna cikin koshin lafiya kuma ana kokarin hada su da iyalansu.
Asali: Legit.ng
