Zuwan Kwankwaso Kano: Jami'an tsaro sun soma shiga jihar domin tabbatar da tsaro (hotuna)
Rahotanni sun kawo cewa jami’an tsaro sun fara shawagi a jihar Kano domin tabbatar da tsaro a jihar.
Hakan ya biyo bayan ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke shirin kaiwa jihar.
Idan zaku tuna a baya Legit.ng ta rahoto cewa rundunar yan sandan jihar Kano ta gargadi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya dakatar da ziyarar da ya shirya kaiwa jihar Kano a ranar 30 ga watan Janairu.
Kwamishinan Yan sandan jihar, Rabiu Yusuf ne ya bayyana haka ga manema labarai, idan yace matukar Kwankwaso ya dage akan shiga jihar, toh lallai doka za tayi aiki akansa, don kuwa zai gamu da fushinsa.
KU KARANTA KUMA: Jiragen ruwa 33 cike da man fetur, da kayayyakin abinci na shirin isa Lagas
Sai dai tsohon gwamnan, ya bayyana cewa babu wanda zai iya hana shi zuwa mahaifarsa.
Inda tsohon gwamnan yake cewa, zai ziyarci jihar ne lami lafiya ba tare da wata tarzoma ba domin ganawa da 'yan uwa, makusanta da abokai da aka jima ba a gana da juna ba.
Ga karin hoto a kasa:
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng