Yan uwa 2 sun Musulunta bayan yayarsu ta karbi Musulunci a jihar Imo (hotuna)
- Yan uwa biyu sun Musulunta a jihar Imo
- Yan uwan biyu sun Musulunta ne bayan yayarsu ta karbi addinin Musulunci
Legit.ng ta ci karo da labarin yan uwa biyu da suka Musulunta. Yan uwan biyu da aka ambata da suna Chijoke da Chiamaka Obi wadanda suka kasance Kiristoci sun musulunta ne a jihar Imo.
An tattaro cewa yan uwan biyu sun karbi Musulunci ne bayan yayrsu mai suna Aishat Obi ta rigada ta karbi Musulunci. Legit.ng ta ci karo ne da labarin bayan yar uwar tasu wacce ta kasance Musulma ta yada a shafin Facebook.
Aishat wacce ta yada labarin a shafinta tayi godiya ga Allah da aka amcesu cikin Musulmai a jihar Imo.
Ta kuma bayyana sunayen kannen nata na Musulunci a matsayin Rahman Obi da Rashidat Obi.
KU KARANTA KUMA: Ban yi danasanin tattakin da na yi lokacin da Buhari ya ci zabe ba – Inji Suleiman Hashimu
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng